Mabambantan Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Nijeriya Kan Jawabin Shugaba Buhari

0
100

Ose Anenih, “Mun gamsu da shugaban kasa Buhari a matsayin jarumin wanzar da demokradiyya domin kuwa domin ya nuna mun gani muna kuma shaida irin salon nasa,”

Ali Ashirun ya ce, “Buhari ka yaudari kanka da har kake misalta farashin Mai da Saudiyya. Alfashin mafi karancin ma’aikaci a Saudi nawa ne? Ka bani mamamaki wallahi. Ba ku dai son talaka ya ji dadinku Sam,”

Mabambantan Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Nijeriya Kan Jawabin Shugaba Buhari

Muhammad Gambo, “Tabbas Buhari na bukatar karin uzurin ‘yan Nijeriya. mu fara duba inda ya amshi mulki da irin tarnakakin da ke gabansa. Buhari na son gyara amma matsalolin photo voltaic masa dabaibayi, abun da na fahimta da maganganun shugaban kasa a wannan rana wani salo ne na sake farfado da Nijeriya. muna murnar zagayowar wannan rana,”

Faruk Gangaran (@FarKay_) ya ce, “Buhari da shi da wanda ya rubuta masa wannan jawabin photo voltaic nuna mana cewa koda farashin Mai zai kai naira dari uku za su ci gaba da neman uzuri da ba mu bayanin rarrashi don neman uzurta musu. Abun kaito da takaici wallahi! Muna da jan aiki a gabanmu.”

Idris Saidu, “Koma dai menene da ya ke tarihi na nan a rubuce, komin dadewa wasu za su karanta cewa lokacin shugaban kasa wane an yi kaza da kaza, in na kirki ne su ce Allah jikansa, Yai mashi afuwa kamar yadda ake wa Ummaru Yar’adua, in akasin haka ne su yi mugunyar addu’a. Allah kyauta, Ya gyara shugabanninmu, Yai masu jagoranci,su zan masu tausayinmu da jinkanmu, ameen.”

Kalli Zafafan Bidiyon Fati Washa Na Murnar Ranar Samun ‘Yancin Najeriya

Shi kuma dai Tosin (@Donteewrites) “Wannan jawabin na Buhari shine mafi munin jawabi cike yake da surkulle,”

Shi kuwa Karo (@Karoboni) cewa ya yi, “Jawabin Buhari na ranar ‘yancin kai yaudarar ‘yan kasace muraran a ciki.”

Lawan S. Zazzau ya ce, “Ranar ‘yanci kai babu wani dalili da zai sa na zagi kasata ta saboda tana da tarin arziki amma bai kara so gareni ba. Sai dai na yi wa wadanda alhakin tafiyar da arziƙin kasar yake a hannun su addu’a Allah ya shirye su.”

Ya ce, Buhari ya amshi mulki ne a daidai lokacin da kasar ke cike da rashawa da suka yi wa rassa dabaibayi kana suka durkufar da tattalin arzikin jihar kana ita ma annobar Korona ta zo ta kara lafta nata kalubalen wajen gurgunta tattalin arziki.

Ya ce, Buhari na da zimmar da himmar ciyar da kasar nan gaba illa dai kalubalen da suka mamaye shi.

Don haka ne ya nemi ‘yan Nijeriya da su mara baya dari bisa dari domin baiwa shugaban zarafin saita kasar nan da sauran shekarun da ke da su a kan mulki.

What's On Your Mind?