Ma’aikatar Jinkai Za Ta Yi Amfani Da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Wajen Raba Tallafi

0
145

Ma’aikatar Jinkai Za Ta Yi Amfani Da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Wajen Raba Tallafi

Daga Maigari Abdulrahman,

Hukumar jinkai ta kasa ta ce za ta fara anfani da kungiyoyi masu zaman kansu wajen raba tallafi ga al’ummma domin tabbatar da daidaito da adalci.

Hajiya Sadiya, Ministar jinkai ce ta bayyana hakan a yayin wata ganawa kwamitin ‘yan majalisar tarayya kan manyan harkoki, a Abuja ranar Alhamis.

Ministar, wacce ta koka da rashin samun rahoton kasafin tallafin Covid-19 daag jihohi, ta ce  akwai bukatar hukumar ta sake fiddo da sabbin tsare-tsare don sa ido da tabbatarwa.

“Har yanzu ba mu samu rahoto daga kowane gwamna ba kan yadda su ka rarraba kayan tallafin Covid-19, hakan ya sa muke tunanin anfani da kungiyoyi masu zaman kansu nan gaba,” in ji ta

Ta ci gaba da cewa, “tunda har yanzu ana kan ci agba da ayukkan Covid-19, akwai bukatar fitowa da sabbinb hanyoyi don ganin tallafin ya riski mabukata.”

Ta bayyana cewar, adadin kudi 2,457,500,000 aka fitar ga hukumar na tallafin Covid-19, wanda  a ciki ta ce, har yanzu biliyan 30 ba su shigo hannun su  ba.

“Wannan kudin tallafi ne zuwa ga mabukata miliyan daya, kowa dubu 5 na tsawon wata 6,” in ji ta.

Dangane da ciyar da ‘yan  makaranta kuwa, ta ce solar ci gaba daraba abincin har a lokacin kullen Covid-19, inda ake kai abincin a gidajensu a maimakon makaranta.

“Gwamanti ta umurci da mu ci gaba da tsarin ciyarwa har a lokacin kullen. Muna da bayanan daliban da gidajensu, kam haka sai aka ci gaba da riskarsu a gida,” in ji ta.

Dangane da shawagin jirgin sama, ta ce solar yi anfani da jirgin sama a Abuja, Legas da kuma Ogun. To sai dai, ba a cigaba ba sakamakon wasu matsaloli da aka fuskanta.

Tun a farko, shugaban kwamitin, Sanata Yusuf, ya bayyana cewar, tabbatar da gaskiya ne manufar ganawar ba cin fuska ko kure ba. Manufar ita ce bincikar kwamitin fadar shugaban kasa na Covid-19, hukumar jinkai da ma’aikatar agajin gaggawa kan yadda su ka gudanar da aikinsu, kamar yadda dokar kasa ta umurta.

What's On Your Mind?