Ma’aikata Ku Ci Gaba Da Ba Da Gudummawa Don Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya – Hon Zailani

0
51

Ma’aikata Ku Ci Gaba Da Ba Da Gudummawa Don Habaka Tattalin Arzikin Nijeriya – Hon Zailani

Daga Abubakar Abba,

Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar Kaduna Rt Hon Yusuf Ibrahim Zailani ya jinjinawa  daukacin ma’aikatan da ke a fadin kasar nan bisa gudunmawar da suke ci gaba da bayar wa wajen habaka tattalin arzikin Nijeria.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da  ta samu sa hannun shugaban ma’aikata ga a shugaban majalisar Haruna Jafaru Sambo ya san ya hannu.

Zailani wanda kuma shi ne, shugaban kungiyar shugababnin majalisun dokokin Arewacin Nijeriya ya yi yabon ne kan bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a daukacin fadin Nijeriya a jiya Asabar.

Shugaban wanda kuma  har ila yau shi ne Chiroman dan Darman Zazzau ya ce, “ ‘Yan Nijeriya  da kuma Nijeriya na tunkaho da ma’aikatan kan zagewar su wajen yin aiki tukuru, ina kuma mai baku shawara da ku kara zage wa wajen yin aiki domin kara ciyar da Nijeriya da kuma tattalin arzikinta gaba.”

Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar ya kuma nuna jin dadinsa kan gudunmawar da ma’aikatan majailsar  da kuma hukumar ma’aikata ta jihar kan goyon bayan da suke bai wa majalisar da ke a jihar.

 

Yusuf Ibrahim Zailani ya kuma nuna jin dadinsa kan yadda jami’an tsaro a kasar nan suke ci gaba da yin aiki  tukuru wajen yakar ayyukan ‘yan ta’adda a daukacin fadin kasar nan.

 

“Dole ne  a yaba wa jami’an tsaron kasar nan kan ci gaba da suke yi da  yakar ayyukan ‘yan ta’adda a daukacin fadin kasar nan”.

 

Shugaban Majalisar  ya kuma yaba wa jami’an kiwon lafiya da ke a daukacin fadin kasar nan wajen dakile yaduwar annobar Korona.

A wata sabuwa kuma, Shugaban ya bayar da kyautar bas kirar Toyota Coaster mai cin mutum 22 ga Gidauniyar

Zailani Absolute Care.

A cikin sanarwar  Hadimin sa Ibrahim dahiru danfulani  ya ce, Zailani wanda kuma shi ne uban Gidauniyar, ya gabatar da kyutar bas din ce a wani taro da shugaban ma’aikatansa ya Haruna Jafaru Sambo ya walice shi.

Ya kuma yi kira ga shugabain Gidauniyar da su yi amfanin da bas din bisa yadda  ya dce.

Da yake karbar bas din a madadin Gidauniyar Kwamarade Tasiu Musa, ya bayar da tabbacin  cewa, za a yi amfani da bas bisa yadda ya da ce domin amfanin daukacin alummar da ke a jihar.

What's On Your Mind?