Lokaci Ya Yi Da Gwamnatin Buhari Za Ta Sauya Salonta –Okorocha 

- Advertisement -

Lokaci Ya Yi Da Gwamnatin Buhari Za Ta Sauya Salonta –Okorocha 

Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha ya bayyana cewa rashin adalci da yaduwar talauci su suka haddasa tsanan mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Okorocha wanda shi ma mamba ne daga cikin jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne lokacin da yake tarbar bakoncin tawagar wasu musulmi da suka kai masa ziya a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata. Tsohon gwamnan Jihar Imo ya kara da cewa, gwamnatin tarayya wacce jam’iyyar APC take jagoranta dole ne ta dauki matakan magance rashin adalci da yakan talauci, domin dawo da martabanta a idanuwan ‘yan Nijeriya.

Okorocha ya ce, “na tabbatar da cewa kashe 75 na ‘yan Nijeriya ba sa jin dadin abubuwan da suka faruwa. Babu wani abun da za a iya tabukawa a wannan kasa idan har yawan mutane ba sa jin dadin abubuwan da ke faruwa. Ya kamata mu tashi tsaye wajen dawo da jin dadin da walwala a cikin wannan kasa.

“Ba za ka iya magance matsala ba har sai idan ka san tushinsa. Matsalolin da ke damun kasarmu Nijeriya dai su ne, rashin adalci da talauci, dole ne gwamnati ta yi kokarin yakar rashin adalci domin rage yawan tushin da ake da shi a cikin kasar nan.”

Haka kuma ya karfafa wa ‘yan Nijeriya kwarin gwiwa a kan kar su yanke zato ga kasarsu, domin nan ba da jumawa ba za a samu sabuwan Nijeriya, saboda abubuwan za su daidaita.

- Advertisement -