Liverpool Za Ta Iya Rasa Gurbin Zakarun Turai

- Advertisement -

Liverpool Za Ta Iya Rasa Gurbin Zakarun Turai

Daga Abba Ibrahim Wada

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya ce akwai alamun ba za su iya samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa ba, saboda yadda kungiyar ke ci gaba da zama a matsayi na 7 yanzu haka a teburin gasar Firimiya ta Ingila.
Yanzu haka kungiyar wadda ta lashe gasar firimiya a shekarar knowledge gabata ta na da maki 54 da kwantan wasa guda daya a karawar da aka soke tsakaninta da kungiyar Manchester United, kuma idan ta samu nasara za ta iya komawa matsayi 6.
Ganin cewa yanzu haka saura wasanni hudu a kammala gasar baki daya, Klopp ya ce kungiyar sa da ta lashe gasar bara na cikin mummunan yanayi sakamakon matsalolin da ta fuskanta bana wajen raunin da fitattun ‘yan wasan ta suka fuskanta.
Daga cikin ‘yan wasan da kungiyar ba ta ci moriyarsu sosai ba a wannan kaka saboda rauni har da mai tsaron bayanta lamba daya wato birgil ban Dijk da Joe Gomez da Joel Matip da kuma kaftin dinta Jordan Henderson.
“Tabbas abubuwa solar lalace mana tun farkon fara wannan gasa kuma munyi kokarin magance matsalar tun kafin tayi nisa amma bamu iya samun nasara ba saboda mun makara wajen yin gyaran” in ji Klopp
Ya ci gaba da cew “Amma duk da haka zamu ci gaba da neman nasara a ragowar wasannin mu na gaba wanda idan muka samu nasara a ragowar wasannin mu zamu iya canja wasu abubuwan”
Halin da kungiyar ta samu kan ta a yau na nuna cewar watakila wasan da za ta yi a Turai a kaka mai zuwa zai zama na Europa League ne saboda ganin manyan kungiyoyin da ke gaban ta yanzu haka a teburin Firimiya.

- Advertisement -