Lewandowski Ya Warke Kuma Zai Fara Buga Wasa

0
61

Lewandowski Ya Warke Kuma Zai Fara Buga Wasa

Dan wasa Robert Lewandowski ya warke kuma ya koma filin daukar atisaye a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ranar Laraba, bayan jinyar kusan wata daya da dan kasar Poland din ya yi.

A yau Asabar ake sa ran Bayern za ta lashe kofin Bundesliga na kuma tara a jere, idan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Mainz a gasar Bundesliga kuma ana saran kociyan kungiyar zaiyi amfani dashi.

dan kwallon tawagar Poland din, mai shekara 32 a duniya ya koma atisaye, bayan jinyar raunin da ya yi a gwiwar kafarsa a lokacin da yake buga wa kasarsa wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za’a buga a shekarar 2022.

Tuni kocin Bayern, Hansi Flick ya ce yana fatan Lewandowski zai ci gaba da cin kwallaye, domin kamo tarihin tsohon dan wasan kungiyar, Gerd Muller wanda ya zura kwallaye 40 a raga a kakar wasa ta shekarar 1971 zuwa 1972.

Lewandowski wanda ya ke da kwallaye 35 a raga a kakar bana, kuma saura karawa uku a kammala wasannin Bundesliga na bana ya ce bai sani ba ko zai iya doke tarihin da Muller ya kafa a cikin wasannin da suka ragewa kungiyar.
Haka kuma shima dan wasa Serge Gnabry ya koma karbar horo, bayan da ya kammala killace kansa, sakamakon kamuwa da cutar korona har ila yau, shima dan wasa Corentin Tolisso ya koma atisaye, bayan jinya da ya yi.

What's On Your Mind?