Lawan Garba Bullet Ya Yaba Wa Ganduje Kan Kulawa Da Harkokin Mata

0
89

Lawan Garba Bullet Ya Yaba Wa Ganduje Kan Kulawa Da Harkokin Mata

Daga Ibrahim Muhammad,

Dan majalisa mai wakiltar Garki a majalisar haha Jigawa Hon. Garba Lawan  Bullet  ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi  Umar Ganduje bisa kulawa da take baiwa cigaban Mata ta basu dama wajen sanyasu a manyan mukamai.

Dan majalisar wanda ya bayyana hakan yayin da aka raka Hajiya Amina Muhammad Usman don kama solo a matsayin sabuwar babbar sakatariya a ma’aikatar sufuri da gidaje na jihar Kano.

Ya yi nuni da cewa irin rawar da yake takawa wajen baiwa Mata dama zai taimaka sosai wajen bunkasa cigaban al’umma duba da yadda Mata suke taka rawa wajen tarbiyar Iyali da tausayi za su yi duk abinda yakamata wajen ciyar da al’umma gaba.

Hon. Lawan Garba Bullet  ya bayyana cewa Babbar sakatariyar  mace  mai kwazo da aiki tukuru wanda hazakarta ce take samun cigaba da daukaka a fagen aikinta. Sannan ya jaddada kira a gareta wajen cigaba da aiki tukuru da riko da gaskiya da amana da taimakawa cika  buri da manufar Gwamna  Ganduje na bunkasa jihar Kano musamman a fannin Sufuri da gidaje.

Hajiya Amina Muhammad  Usman ta ce za su hada karfi da karfe  rattling sauran  ma’aikata don bunkasa cigaban ma’aikatar da jihar Kano,ta Kuma gode wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje  bisa irin kokarin da yake wajen bunkasa cigaban jihar Kano.

What's On Your Mind?