Lalata Dangantaka Tsakanin Sin Da Afirka Da Amurka Ta Yi Ba Zai Samu Nasara Ba

- Advertisement -

Lalata Dangantaka Tsakanin Sin Da Afirka Da Amurka Ta Yi Ba Zai Samu Nasara Ba

Daga CRI Hausa

A kwanan nan ne sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya mai da hankalinsa kan nahiyar Afirka, inda ya gudanar da shawarwari ta kafar bidiyo da shugabanni gami da ministocin harkokin wajen Najeriya da Kenya, da tattaunawa da daliban Afirka wadanda suka taba karatu a Amurka, a wani yunkuri na lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da ci gaba da yayata raayoyin da suka shafi barazanar Sin da tarkon bashi da kuma bayyana cewa wai alummar kasar Sin solar kwace damammaki daga mutanen Afirka. Amma hakikanin gaskiya ita ce, Sin da Afirka solar cimma dimbin nasarori wajen karfafa hadin-gwiwarsu. Yunkurin lahanta dangantakar, ba zai ci nasara ba.

Babu gaskiya cikin kalaman bangaren Amurka ko kadan, balle makama. A yayin da yake amsa tambayoyin da matasan Afirka suka yi masa, Antony Blinken ya ce, Amurka ba ta bukatar a yi zabi tsakaninta da Sin, amma tana fatan Afirka za ta lura da fadadar tasirin kasar Sin a duniya, yana mai shafa wa gwamnatin kasar Sin bakin fenti cewa, wai zuba jarin da ta yi a fannin gina muhimman ababen extra rayuwa gami da bayar da basussuka ga kasashen Afirka, ya sa solar tsunduma cikin matsalar rashin samun ci gaba mai dorewa. A nasa bangaren kuma, mukaddashin mai taimakawa sakataren harkokin wajen Amurka wanda ke kula da harkokin Afirka, Robert Godec ya kara da cewa, wai kasarsa za ta nunawa alummar Afirka cewa, Amurka tana kara maida hankali kan moriyar Afirka, idan aka kwatanta da hanyar raya tattalin arziki da kasar Sin ta bi a nahiyar. A wani bangaren, Amurka ta ce wai ba ta bukatar kasashen Afirka su yi zabi tsakaninta da Amurka, amma a dayan bangaren kuma, solar nemi kasashen Afirka su nisanci kasar Sin, su zabi Amurka. Wato ainihin makasudin ita Amurka shi ne, hura wutar rikici tsakanin Sin da Afirka, da kara kwace moriya a nahiyar.

Idan muka waiwayi tarihi, yau shekaru 600 da suka gabata ne, shahararren jami’in kula da alkiblar jirgin ruwa a daular Ming mai suna Zheng He ya taba zuwa gabar tekun dake gabashin Afirka, sannan yau sama da rabin karnin da ya shige ne, injiniyoyin kasar Sin suka je Afirka don taimakawa shimfida wani layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya. Bugu da kari, hadin-gwiwar Sin da Afirka ya kai sabon matsayi a wadannan shekarun baya. Amma mu’amalar kasashen yammacin duniya da Afirka kuma, cike take da tarihin kutsa kai gami da mulkin mallaka.

Tun bayan kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin zuwa yanzu, kasar Sin tana marawa al’ummar Afirka baya a fannin yaki da masu danniya da Turawa yan mulkin mallaka, da kwato ’yanci gami da raya kasa. A halin yanzu, huldar Sin da Afirka tana dada bunkasa cikin sauri. Tun bayan da aka kafa dandalin tattauna hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma FOCAC a takaice yau shekaru sama da 20 da suka wuce, kawo yanzu, jimillar kudin cinikin da aka yi tsakanin Sin da Afirka ta karu har sau 20, kana yawan kudaden da Sin ta zubawa Afirka ya karu sau 100. Muhimman matakai eight da aka sanar a wajen taron koli na Beijing na dandalin FOCAC suna kawo babban alfanu ga al’ummar Afirka, kuma dabarun yaki da fatara na kasar Sin solar kara fadakar da Afirka kan tsara nasu dabaru a wannan fanni.

A yanzu haka dai ana kara mu’amalar al’adu tsakanin Sin da Afirka, kuma akwai matasan Afirka da dama wadanda ke karatu a biranen kasar Sin daban-daban, wadanda kuma suke ganewa idanunsu ainihin halin da ake ciki a kasar ta Sin. Tarihi gami da abubuwan da suke wakana a halin yanzu solar sha jaddada cewa, babbar ka’idar hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka ita ce, samar da moriyar juna. Duk wani yunkuri na shafawa kasar Sin bakin fenti ko kuma lalata dangantakarta da Afirka, sam ba zai ci nasara ba.

A halin yanzu, duniya na fuskantar kalubaloli a fannoni daban-daban, ciki har da sauyin yanayi, da yaduwar annobar COVID-19, da kuma ayyukan ta’addanci, al’amarin da ya bukaci Sin da Afirka su zama tsintsiya madaurinki daya, da ci gaba da inganta hadin-gwiwa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Mai Fassara: Murtala Zhang)

- Advertisement -