Labarin Yadda Masu Garkuwa Da Mutane Suka Jefa Al’ummar Taraba Da Adamawa Cikin Dar-Dar

- Advertisement -


Yau Labarin Mun LekabShafin Bbc Hausa Inda A yayin da sassan Najeriya ke fama da matsalolin tsaro daban-daban, daga rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar da hare-haren ‘yan bindiga a arewa maso yammacin kasar da kuma rikice-rikicen kabilanci a arewa maso tsakiyar Najeriyar, su kuwa jihohin Taraba da Adamawa matsalar satar mutane ke ci gaba da munana a jihohin biyu.

Wannan na faruwa ne duk da ikirarin da jami’an tsaro ke yi na kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.

A cikin wannan makalar, Salihu Adamu Usman, ya duba mana yadda satar mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Taraba da Adamawa.

A ‘yan kwanakin nan da zarar mutum ya zaga wurare da jama’a ke hira a Jalingo fadar jihar Taraba maudu’in da akasarin mutane ke tattaunawa shi ne matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Wannan dai ba zai rasa nasaba da yawaitar satar mutane da ake yi a kauyuka da kuma manyan garuruwa da ke jihar ba.

Ko da yake Taraba ba ta sha fama da hare-haren kungiyar Boko Haram ba kamar sauran takwarorin ta da ke arewa maso gabashin Najeriya, to amma ita ma tana fama da nata matsalolin tsaron.

A gwamman shekaru da suka gabata jihar ta yi kaurin suna wajen rikice-rikicen kabilanci da kuma rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya.

To sai dai kuma a shekarun baya-bayan nan, wata sabuwar matsalar ta kunno kai ma’ana ta satar mutane.

Ko da a ranar Larabar da ta wuce sai da aka sace dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Nguroje Barrister Bashir Muhammad wanda har kawo yanzu babu labarin sa.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, an yi garkuwa da fitattun mutane kamar su mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Haruna Manu, Hajiya Hauwa Belli da tsohon mai magana da yawun gwamnan jihar Hassan Mijinyawa.

Har ila yau, an sace tare da kashe tsohon dan majalisar dokokin jihar da ya taba wakiltar mazabar Takum ta daya Hosea Ibi a shekarar 2018.

Wadannan alamomi ne da ke nuna babu wanda ya isa ya daki kirji cewa zai tsallake tarkon masu satar mutanen sai wanda Allah ya kubutar.

Yadda ake ganawa wadanda aka sace ukuba

Kusan labari iri daya ne za ka rika ji daga bakin duk wadanda aka taba garkuwa da su a jihar Taraba.

Abin da suke furtawa bai wuci irin azabar da barayin suka gana musu ba yayin da suke hannu.

Na tattauna da wani mutumin da ya taba fadawa tarkon masu satar mutane bayan ya sayi gida a hannun su ‘bisa kuskure’.

Malamin ya ce bayan sayen gidan ne sai barayin suka biyo dare suka kwankwasa masa kofa sannan suka tafi da shi cikin daji inda suka ajiye shi a can.

“Da daddare karfe daya da rabi suka shigo, ina bude kofa kenan sai naji mari, suka dauke ni muka kama tafiya nidai gaskiya ban taba tafiya irin wannan ba arayuwa ta,” in ji shi.

Ya kara da cewa akwai cin zarafi iri-iri kamar daure mutum da duka da zagi da rufewa mutum ido da sauran su. “Ko zagawa ka nemi yi dole sai da mutum dauke da bindiga akan ka,” a cewar sa.

An sako wannan malamin ne bayan biyan wasu kudade ga masu satar mutanen.

Mazauna Jalingo na ‘cikin fargaba’

Karuwar matsalar satar mutanen ta ‘jefa tsoro da fargaba’ a zukatan mazauna Jalingo ganin cewa hatta a fadar jihar akan bi mutane har gida cikin dare ana musu dauki dai dai.

Wani dan kasuwa a birnin ya ce “idan mutum na kwance a gida ba shi da kwanciyar hankali, idan zai yi tafiya ma haka ballantana a ce yana so ya sayi wata kadara ya ajiye shikenan sai a zo a ce ai mai kudi ne a sace shi.”

Ita ma wata mata da ke saye da sayarwa a Jalingo ta ce lamarin satar mutanen na sanyaya musu guiwa wajen gudanar da harkokin kasuwancin su.

“Idan an zo an sace mutum sai kaji ana cewa sai an bada miliyoyin Nairori gaskiya irin wannan hali da ake ciki yana tsoratarwa, wata kila yawancin masu saida kaya za su daina saidawa”. A cewar ta.

Satar Mutane a Adamawa:-

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya sha cewa zai magance matsalar masu garkuwa da mutane amma batun yana nema ya gagari kundila

Sannu a hankali matsalar ta fara shafar makwabciyar Taraba ma’ana jihar Adamawa musamman ma kananan hukumomin Furore da Girei da Mayo Belwa.

A can kuwa barayin mutanen solar fi addabar Fulani makiyaya ne tare da tilasta musu sayar da shanu domin biyan makudan kudaden a matsayin fansa.

Baya ga makiyaya kuwa sai fitattun ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da kuma manyan ma’aikatan gwamnati wadanda hatta a cikin Yola fadar jihar ana sanya musu ido tare da barazanar sace su.

Abunda ‘yan sanda keyi a jihohin biyu

Sau da dama rundunonin ‘yan sanda a jihoin Taraba da Adamawa na ikirarin yin iya karfin su wajen magance matsalar, to amma har yanzu ba’a rabu da ita ba.

DSP David Misal shi ne kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba, yace kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya kafa wata runduna da ake kira “Anti Kidnapping” wacce kusan ko wani lokaci tana kan hanyoyi da kuma yankunan da ake satar mutane.

Ya ce baya ga wannan kwamishinan ya karfafawa sashen da ke bibiyar hirarrakin waya da akeyi da barayin mutane domin fahimtar ainihin inda suke da zummar daukar mataki.

Shi kuwa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawan DSP Yahaya Nguroje yace rundunar ta yi hadaka da wadanda zasu taimaka mata wajen zakulo bata gari.

“Mu yi hadaka da ‘yan banga da maharba domin hawa tsaunuka da kuma shiga dazuka a duk lokacin da aka sace mutane domin kubutar da su da kuma dakile matsalar gaba daya, sannan muna bibiyar dukkan kauyuka domin jawo hankalin shuwagabannin al’umma da na addinai da kuma na kungiyoyi domin suma su bada tasu gudunmawa a harkar tsaro,” in ji DSP Nguroje.

- Advertisement -