Labari mai daɗi : Gwamnatin Tarayya ta bude sauran Iyakokin kasar

0
73

Labari mai daɗi : Gwamnatin Tarayya ta bude sauran Iyakokin kasar

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da matakin cewa an buɗe dukkan iyakokin tudu na ƙasar, bayan solar shafe tsawon fiye da shekara ɗaya a rufe.

Cikin tsakiyar watan jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin fara buɗe iyakoki guda huɗu, kafin yanzu a buɗe ɗaukacin iyakokin tudu da ke faɗin tarayyar Najeriya.

Malamai Sun Fara Martani Akan Haukacewar Shahararen Darakta Wasan Kwaikwayo Ashiru Nagoma

A watan Agustan 2019 ne Najeriyar ta rufe kan iyakokinta da nufin daƙile fasa-ƙwaurin musamman shinkafa da kuma makamai cikin ƙasar.

Babban kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta ƙasar, Muhammad Babandede ya shaida wa BBC cewa tuni shugaban ƙasar ya ba da izinin a buɗe duka iyakokin ƙasar.

“Wannan ya yi dai-dai da lokacin da Najeriya ta shiga tarayyar ƙasashen Afirka kan tattalin arziki wanda za ta buɗe iyakarta don a yi kasuwanci kuma a yi zirga-zirgar mutane” in ji Babandede.

Ya ce da farko an buɗe iyakokin Seme da Maigatari da Illela da Nfom a ƙarshen watan Disambar bara.

“Dole ne mu tabbatar da cewa duka waɗanda za su shigo solar biyo ta ƙa’idar iyaka, solar bi da takardar izini kuma kada a tsangwami mutane na karɓar kuɗi wanda ba a yi shi kan ƙa’ida ba” a cewarsa.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa an tanadi ma’aikatan lafiya a kan iyakokin ƙasar da za su riƙa tabbatar da cewa mutane solar bi duka ƙa’idojin cutar korona.

A cewarsa, ma’aikatan za su duba mutane musamman yanayin zafin jikinsu sannan za su tabbatar da ana ba da tazara tare da sa takunkumi domin hana bazuwar cutar.

Ya ce hukuma ba za ta bari waɗanda suka karya ƙa’idojin su samu shigowa Najeriya ba.

What's On Your Mind?