La liga: Kila Atletico Madrid Ta Kafa Tarihi A Bana  

- Advertisement -

La liga: Kila Atletico Madrid Ta Kafa Tarihi A Bana   

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta sake kama hanyar yiwuwar zama zakarar gasar La liga a bana bayan shafe shekaru 7 ba tare da kai kofin gidanta ba, inda ta sake jan tazara tsakaninta da kungiyoyin Actual Madrid da Barcelona wadanda suka shafe shekaru suna lashe kofin.

 

Atletico bayan nasararta kan kungiyar Actual Sociedad a ranar Laraba, yawan tazarar da ke tsakaninta da Actual Madrid wadda ke gurbin ta biyu a teburin gasar ya zama maki biyu, yayinda ita kuma Barcelona ke da tazarar maki daya tal tsakaninta da Actual Madrid.

 

Atletico Madrid dai na tunkarar kofin na 11 ne a tarihi, kuma nasarar ta ta za ta tabbata ne idan har ta yi nasarar wasanninta biyu da suka rage ya yinda wasa na gaba da ke tunkaro kungiyar shi ne karawarta da kungiyar kwallon kafa ta Ossasuna a yau Lahadi 16 ga watan Mayun da muke sai kuma karawarta da Actual Balladolid a ranar 18 ga wata.

 

Shima kociyan kungiyar, Diego Simeone, ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar ‘yan wasansa za suyi iya yinsu domin lashe gasar cin kofin La liga na wannan kakar  ake dab da karkarewa.

- Advertisement -