Kwazon NIS Na Kula Da Shige Da Ficen Kasa Da Tsaron Iyaka

0
77

Kwazon NIS Na Kula Da Shige Da Ficen Kasa Da Tsaron Iyaka

A wata ganawar da ya yi da kafofin watsa labarai, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), Muhammad Babandede ya bayyana irin ci gaban fasaha da hukumar ta samu a matsayin wata hanya ta gudanar da ayyuka cikin sauki kuma a zamanance.

Ya nunar da cewa a wannan zamanin mun kasancewa cikin rayuwa wadda take da ban sha’awa inda fasaha da sadarwa suke taka muhimmiyar rawa, ko bayar da gagarumar gudummawa wajen hana aikata laifuka da kuma shawo kan matsalolin tsaro.

Kamar yadda ya ce sadarwa da fasaha ta zamani za su ci gaba da taimakawa wajen gudanar da harkokin duniya cikin ludufi, musamman ma idan abin ya kasance yana da alaka da yadda ake amfani da ilimi da kuma al’amuran tsaro cikin sauki, na kula da tafiye-tafiyen dan Adam, ko yadda ake kulawa da shige da ficen Nijeriya da wasu kasashe..

Yadda za a samu damar sa ido kan tafiye- tafiyen mutane da kayayyakin su, ita ce babbar matsalar da jami’an tsaro suke fuskanta, wanda kuma hakan ne ya sa ya zama dole, sai an dauki wani mataki da yake bukatar bullo da wasu sabbin hanyoyi da tsare- tsare ta yadda za a shawo kan matsalolin kamar yadda ya dace, na sa ido sosai kan yadda mutane da kayayyaki suke fita ko shiga ta iyakoki.

Dukkan kasashen duniya kamar dai yadda abin yake kasancewa ko wacce tana da nata irin tsarin ko kuma ka’idoji da suka shafi kula da tafiye-tafiyen al’umma da kuma daukar matakin ba-sani-ba-sabo a bakin iyakar kasa. Wannan kuma bai rasa dalili wanda ko dai al’amarin da ya shafi lafiya ko kuma tsaro. Irin hakan ce ma ta sa hukumar NIS ta dauki wasu kwararan matakai a sport da kula da iyakoki musamman ma, lokacin da annobar cutar Korona ta barke, wanda hakan ne ya sa wasu jihohi suka kara maida hankali kan shige da fice na mutane, ya yin da kuma ta bangare daya ana lura sosai da al’amarin tsaron da ya shafi iyakar kasa da kasa.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulda da jama’ana na NIS, DCI Sunday James ta kara da cewa, Hukumar NIS an dora mata alhaki na lura da shige da fice na mutane masu shigowa da kuma fita kasa ta iyakokin da ake amfani da su domin hakan, inda ta hakan ne jami’ai suke gane wadanda suke neman shiga ko fita ta hanyar da bata dace ba.

Wannan yasa ita hukumar ta ci gaba da bullo da wasu tsare-tsare wadanda za a yi amfani dasu wajen sa ido kan yadda za ta aiwatar da ayyukanta, tare da yin la’akari da ‘yancin dan Adam da kuma ‘yancin da kasashe suke da shi na kare hakkokinsu, da kuma tsaro, da ci gaban tattalin arziki, sai kuma yin duk wani abin da zai sa ayyukanta su kasance babu wata tsangwama.

NIS Ta Kafa Karin Sabbin Manyan Ofisoshi Hudu Domin Karfafa Kula Da Iyakokin Kasa

Wannan ya hada da jami’ai su kasance ko wanne lokaci suna a bakin aikinsu, a iyakokin kasa na kan-tudu da filayen jiragen sama da tashoshin teku, da kuma kawata wuraren aiki a duk inda jami’an NIS suke.

Bugu da kari akwai gudunmawar da jami’n na NIS suke badawa wajen samar da tsaro na cikin gida, ta hanyar yin aiki na hadin gwiwa a sashen Arewa maso gabas, da samar da sansanoni na musamman domin kula da iyakokin kasa guda 14 a wurare daban daban, baza jami’an hukumar a kananan hukumomi 774 da ke fadin Nijeriya, sai kuma manyan ofisoshin shiyya guda takwas na hukumar. Ga kuma ofisoshin hukumar a jihohi 36 har da Babban Birnin Tarayya. Akwai kuma manyan katafaran ofisoshi na musamman guda biyar da za su kula da ayyukan iyakoki, ga kuma wurare 114 su ma da ake duba shige da ficen mutane, sai wurare 72 da ake yin sintiri a filayen jiragen kasa da kasa guda 11, da kuma wadanda suke aiki a tasoshin ruwa na Nijeriya 415 wadanda suka kai kilomita 853.

A shekarar 2020 an samu fasinjojin da suka yi shige da ficen Nijeriya ta jiragen sama da suka kai 1,256,652, ta kan-tudu kuma 109,854, yayin da kuma ta ruwa aka samu 213,161, sai kuma masu tafiya da ababen hawa da suke bi ta barauniyar hanya da su ma aka kama 106.

Wannan sharhin da ake yi, wani abu ne da ya nuna cewar shi al’amarin shige da fice a duk fadin duniya yana da matukar muhimmanci da ba da gudunmawa ga tsaron kasa da kuma bunkasar tattalin arziki. B ama kamar lokacin da maganar cutar Korona ta kunno kai, wanda hakan ta sa kasashe suka sake daukar tsaurarran mataki da suke sa ran za su taimaka musu wurin dakile yaduwar cutar.

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) za ta ci gaba da kasancewa mai ba da gudunmawa wajen gudanar da aikinta na kulawa da tsaron iyakokin Nijeriya, da kuma yadda mutane suke shige da fice, wannan kuma za a yi shi ne ta hanyar samar da jami’ai da amfani da fasahar zamani, tare da hadin gwiwa na kasa da kasa. Wani abu kuma wanda zai matukar taimakawa shi ne horas da jami’anta lokaci zuwa lokaci, domin a tabbatar da ci gaba da kula da iyakokin Nijeriya kamar yadda ya kamata.

What's On Your Mind?