Kwanan Nan Za A Kawo karshen Mastalar Tsaro A Nijeriya –Babban Sufeton ‘Yan Sanda

- Advertisement -

Kwanan Nan Za A Kawo karshen Mastalar Tsaro A Nijeriya –Babban Sufeton ‘Yan Sanda

Daga Bello Hamza,

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya, Mr Usman Baba, ya tabbatar wa da al’ummar Nijeriya cewa, matsalolin tsaron da ake fuskantar a kasar nan za su zo karshe nan ba da dadewa ba.

Ya bayyana haka ne a bikin yaye jami’an ‘yan sanda da aka yi a makarantar horas da ‘yan sanda na Jos ‘Police Employees School Jos’.

Baban sufeton ya samu wakilcin, mataimakin shugaban ‘yan sanda DIG, Mr Danmallam Mohammed, ya kuma ce, zai tabbatar da an samu zaman lafiya kamar yadda ake a da a fadin kasar nan.

Ya kuma yi alkawarin samar da ingantaccen rundunar ‘yan sanda da za su tabbatar da tsaro a dukkan lunguna kasar nan ba tare da wani matsala ba.

Ya kuma kara da cewa, horasa da jamai’a na daga cikin hanyoyin da ya shirya cimma wanna burin nasa na samar da tsaro a fadin tarayyar kasar nan.

Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan goyon bayansa ga rundunar ya kuma yi masa alkawarin cika dukkan alkawarin sa na ganin an samar da tsaro a fadin kasar nan.

 

- Advertisement -