Kwamitin Shari’a Da Dokoki Ya Fara Sauraren Masu-ruwa-da-tsaki  A Kebbi

0
40

Kwamitin kula da harakokin Shari’a da kuma dokoki na jihar kebbi a majalisar Dokoki a karkashin jagorancin Mamba Mai wakiltar Bunza, Barista Aminu Muhammad photo voltaic fara sauraren masu ruwa da tsaki Kan shari’a da Dokokin jihar ta kebbi a jiya a dakin gudanar da taro na majalisar Dokokin jihar kebbi kan su bada shawara ko gudunmuwa wurin tabbatar da an yiwa dokokin manyan laifufuka gyran fuska a jihar.

Kwamitin Shari’a Da Dokoki Ya Fara Sauraren Masu-ruwa-da-tsaki  A Kebbi

An gudanar da zaman ne a dakin gudanar da taron na majalisar dokoki ta jihar kebbi da ke a Gwadangaji a Birnin-Kebbi a jiya .

Bisa ga hakan ne Babban jojin jihar, maishari’a Suleiman Muhammad Ambursa tare da dukkan Alkalan manyan kotukan jihar ta kebbi domin bada tasu gudunmuwa ga gyaran dokokin manyan laifufuka da kuma na tsarin aiki a duk kotuka da kuma hukunta masu laifi kai har da tara yayin kama mai-laifi da aikata laifin a gaban kotu.

Maishari’a Suleiman Muhammad Ambursa ya bayyanawa kwamitin na majalisar dokokin jihar ta kebbi cewa” shi ne shugaban kwamitin rubuta bukatar neman gyaran fuska ga wasu dokokin jihar musamman na manyan laifufuka da gwamnatin jihar ta kafa, saboda haka idan duk abin da suka rubuta da kuma sharawar da suka bayar a cikin kudurin da gwamnatin jihar kebbi ta aikewa majalisar ta dokoki an yi aiki dashi babu shakka za a kara samun sauki wurin aikata miyagun da manyan laifufuka kamar fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma aikata laifin fyade da sauransu.

“Saboda haka muna kara kira da kuma roko ga majalisar dokoki ta jihar da suyi amfani da shawarwarin da aka rubuta a cikin kudurin na neman yin gyara ga wannan dokokin, inji Babban jojin jihar kebbi maishari’a Suleiman Muhammad Ambursa yayin da yake a gaban kwamitin majalisar dokoki mai kula da harakokin Shari’a da kuma gyara ga dokar kotutuka.”

Bugu da kari  nemi kwamitin da su gaggata kammala gyaran dokokin domin mafi a kasarin jahohin kasar nan photo voltaic kammala gyaran dokokin su har photo voltaic soma aiki a kotutuka jahohin, amma a jihar kebbi tsofafin dokoki ne ake amfani dasu wanda idan aka aitaka wasu nau’in sabbabin laifufuka ba a iya yanke hukuncinsu saboda rashin babu doka mai magana kan laifin da aka aikata .

Yan Wasan Kwaikwayon Kannywood Sun Kaddamar Da Shagalin Bikin Tunawa Da Ranar’ Yancin Najeriya

Ya kara da cewa” idan majalisar dokoki ta amince da bukatotin da aka gabatar a gaban kwamitin ya zama doka jihar kebbi zata kara samun zaman Lafiya da kuma kudaden shiga ga jihar, inji maishari’a Suleiman Muhammad Ambursa a gaban kwamitin majalisar dokoki masu kula da harakokin Shari’a a karkashin jagorancin Mamba Mai wakiltar Bunza, Barista Aminu Muhammad.”

Har ilayau domin ku san cewa a gidan Shari’a tsintsiya madaurinki daya muke kuma maganar mu duk gudace shi ne yasa kuka gan duk masu Shari’a a manyan kotunan jihar kebbi su a wannan zauren domin nuna goyon bayansu ga wannan gyaran fuska da za a yiwa dokokin nan. Ya ci gaba da cewa duk abin da kuka ga mun rubuta a cikin kudurin yana da matukar muhimmacin saboda haka shawara ta a nan shi ne kada a cire komai daga cikin domin duk suna da amfani da kuma muhimmacin gaske.

Saboda haka Ina godiya ga damar da aka baiwa gidan Shari’a domin bada gudunmuwar mu ga wannan gyara da ake son tabbatar wa a wannan jaha ta kebbi.

Da ya ke jawabinsa tun farko, shugaban kwamitin kula da harakokin Shari’a da dokoki Barista Aminu Muhammad Bunza ya bayyanawa Babban jojin jihar da kuma sauran manyan Alkalan jihar ta kebbi cewa” saboda samin muhimmacin ku ga abin da ake son tabbatar wa shi ne yasa kwamitina ya aike muku da takardar gyata domin ku bada shawarwari ko kuma gudunmuwar domin a cinma nasara gyaran wannan dokokin, inji shugaban kwamitin Barista Aminu Muhammad Bunza yayin da yake karbar bakuncin Babban jojin jihar tare sauran manyan Alkalan jihar ta kebbi a zauren majalisar dokoki”.

Haka kuma shugaban ya basu tabbacin cewa duk abin da suka rubuta ko kuma suka bayar a tsayar shawara wannan kwamiti zai yi aki dashi domin shi ne nasarar mu da kuma al’ummar jihar kebbi domin mu wakilan jama’a ne, sannan kuma gidan Shari’a photo voltaic fi kowa sanin abin da ya kamata a yi domin magance wasu matsaloli ga aikata miyagun laifufuka da kuma gyaran dokoki manyan laifufuka na jihar domin ku ne ke fama da masu aikata laifi a gaban kotutukan jihar nan.

Bisa ga hakan kwamiti da kuma sauran mambobbin majalisar dokoki ta jihar za muyi iya kokarin mu na ganin cewa mun yi abin da zaya amfani mutanen mu da kuma kotutukan jihar kebbi da sauransu.
Daga karshe Ina bada tabbacin cewa dukkan shawarwari da kuma gudunmuwar da muka  samu daga sauran jama’a da kuma kungiyoyin na gwamnatin da masu zaman kansu duk zamu yi aiki da su domin cinma nasara abin da ake son.

What's On Your Mind?