Kutsen ‘Yan Ba-ni-na-iya Ga Tafiyar Da Mulkin Jihar Yobe

0
142

Kutsen ‘Yan Ba-ni-na-iya Ga Tafiyar Da Mulkin Jihar Yobe

Daga Maitela

Adawa a tafarkin dimukuradiyya ita ce gishiri kuma kadarkon da tsarin siyasa ke tafiya wanda ya dace a samu a kowane mataki, sashe ne da ya ke taka muhimmiyar gudumawa da amfani da yanayi wajen dakile kafar da jam’iyya mai mulki ke kokari saboda kar yan adawa su ga gazawa da toshe bakinsu a tafiyarta. Sannan kuma rashin adawa ko gazawa a gefen babban cikas ne wanda yake jefa tsarin cikin watangarereniya da jawo hannun agogo baya wajen yi wa jama’a aiki da aiwatar da muhimman kuduriri da manufofin da ya dace su samu a tsarin.

Bugu da kari, idan wannan muhimmin jigo ya samu tazgaro, tsarin ya gamu da cikas tare da samun babban gibin da babu mai cike shi sai “hannu na hudu” a tsarin dimukuradiyya (‘yan jaridu), wanda shi ma a hakikanin zahiri bai faye aiki ba idan bai samu cikakken goyon bayan bangaren adawa ba a tafiyar. Yayin da bisa ga ittifakin masana a tsarin solar bayyana cewa rashin adawa mai karfi da gazawar sashen yana daga cikin ummul haba’isan da jawo dimukuradiyya ke samun kwan-gaba kwan-baya a kasashen Afrika.

Haka zalika, ta la’akari da wannan batu a siyasar Nijeriya, rashin adawa ko gazawar yan adawa wajen amfani da makamashin da suke dashi domin zaburar wa tare da raya tsarin kana ya gudana bisa kafafun sa na asali, wanda hakan ke mayar da hannun agogo baya a tafiyar, rashin armashi da katabus da zai firgita bangaren mulki a fannin aiwatar da muhimman ayyuka ga yan kasa- an wayi gari zai yi wuya a bambance jam’iyyar adawa da mai mulki a idanun talakan kasa, duk inda ya juya babu sa’ida.

Har ila yau kuma, an kirkiro jihar Yobe ne ranar 27 ga watan Augustan 1991- kuma tun bayan komawa zuwa tafarkin dimukuradiyya, siyasar jihar ta na tafiya a karkashin jam’iyyar mai mulki (duk jam’iyyar da ta kafa gwamnati a haka za a tafi- kowa ya bi) har zuwa jam’iyyar APC a matsayin ita ce wadda ta samu damar baza karfin fada aji a wannan salo na jam’iyya falan-daya (mai kama da: One Occasion System), wanda duk da ba a ce babu wasu jam’iyyu ba, amma basu wuce jeka-na-yika bane, wanda hatta jam’iyyar PDP a zahiri suna ce, ba ta da wani fada a ji balle tasirin adawarta ya firgita jam’iyya mai mulki da gyara zamanta- ta ga dama ta rinka yawonta ko dan kamfai babu.

Bugu da kari, duk da idan bai bibiyar shafukan sadarwa na zamani, mutum zai rantse da Allah akwai adawa, wanda yanayin siyasar jihar ya shafe tasirin su ko wani katabus, musamman a wannan karo na dokin mai baki ya fi gudu, lokaci mai kama da na damisar kwali, wanda ko shakka babu ga duk wanda ya san siyasar Yobe, babu adawa face kawai adawa ta mummunar gaba, tuggu da babakere a tsakanin ‘yan jam’iyya mai mulki ta APC- maimakon ‘yan adawa sai ya zama su ne ‘yan adawa kuma masu mulki- kura ta ci kure, sabanin yadda yake a tsarin dimukuradiyya.

A hannu guda kuma, su kansu ‘yan siyasar solar san da wannan tare da furta cewa wannan adawa da gaba solar samo asali ne bisa ga yanayin irin yadda shugabani da masu fada aji a mulkin jihar, a karkashin jam’iyyar APC suke tafiyar da abubuwa a dukunkune, sannan da bin son rai, suka zuba ido har aka wayi gari ‘yan bani-na-iya suka yi wa kowane lungu da sakon gwamnatin kutse, wanda hakan ya basu damar daukar matakan amfani da damar da ta zo musu babu tsammani wajen dakile wa wasu da suka cancanta hanyoyin samun nasarar wasu mabiya, saboda kusancin su da masu mulki, ko da mabiyan jam’iyyar APC solar samu nasara suna iya lalata nasarar ta hanyar hana ta aiki a zahiri.

Mai karatu zai yarda da ni idan zai yi la’akari da fuskokin da suka yi kane-kane a wannan gwamnati ta jihar Yobe, zai sha mamaki saboda mafi yawan sabbin fuskoki ne ‘yan bani-na-iya wadanda wasu daga cikin su bai wuce a kira su da ‘yan nanaye ba, wasu solar zo bayan nasarar zaben 2019 yayin da wasu a gefe suke sai bayan komai ya kankama suka shigo. Akwai korafi sosai a bakunan wadanda suka sha wahala a baya, tare da tambayar cewa: shin dama akwai wadannan fuskokin tun can da, a ina suka yi layar zana, ba su tashi bayyana ba sai a lokacin girbi?. Sannan kuma baya ga duka har da tsinka jaka: kura da shan duka gardi da kwasar kuddi, an bar masu wahala suna fama da garjin rana, babu wata alfatma balle ba su damar bayar da gudumawa don ci gaban jihar da al’ummar ta, ‘yan bani-na-iya solar shiga solar fira su ne neman mukamai ko ta halin kaka, kwangila, jari ko tallafi na musamman a hannun gwamnatin ba su damu da gina jihar Yobe ba. Kuma da yake dokin mai baki ya fi gudu, tuni hakarsu ta cimma ruwa a fannin fada a jji, wanda ko wani ya samu dama (idan ba su ne ba) solar rinka kai gwauro mari wajen bata shi da dakile karsashin bayar da gudumawar jawo ci gaba a jihar.

Masu fashin baki a zamantakewa tare da kimiyyar siyasa solar bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga kowace gwamnati ko duk shugaba mai hangen nesa saboda irin wannan tafiyar: ana tubka baya tana warwarewa a siyasance da gwamnatance, wanda bayan an samu nasarar matsayi komai tsananin rabo hakan zai iya kai wa ga matakin dakile tasirin nasarorin da ya samu aiki, saboda yadda ‘yan bani-na-iya za su hana ruwa gudu a gwamnatinsa, wanda a karshe za a yi babu tsuntsu babu tarko.

Har ila yau, ko da gwamnatin jihar Yobe ta yi nasarar hana tasirin ‘yan adawa a siyasance, wannan kutse na ‘yan bani-na-iya zai iya samar da makeken gibin syasar gaba tsakanin yan jam’iyya mai mulki masu kwazo da hangen nesa da ‘yan a bi Yerima a sha kida tare da mayar da hannun agogo baya a nasarar da gwamnatin ke ikirarin ta samu, saboda abu ne mai a samu dorewar nasara a irin wannan yanayi wanda ko shakka babu babban kalubale ne. Wannan yanayi ne ya tabbatar da cewa akwai wadanda solar ddauki tsawon lokaci suna neman kafa kowace iri ce a gwamnatance kuma ga alama hakar su ta cimma ruwa.

Wanda bisa ga halin da ake ciki, ‘yar manuniya ta tabbata tare da bayyana manufofin su a fili, wanda zancen da ake ciki yanzu a jihar, ‘yan bani-na-iya solar yi matukar tasiri tare da baza fika-fikansu wajen hana ruwa gudu a jihar Yobe- wanda ana iya cewa kusan komai yana neman ya tsaya a jihar amma ko a kwalar su. Dama ta samu ga irin wadannan mutane, illa iyaka su gina kansu sai iyalin su da ‘yan uwansu da wani bangare na abokansu, karawa ma da karau, wasun su solar fice zuwa wasu jihohi don ci gaba da gina kansu da dukiyar jihar, ba tare da la’akari da halin da jihar ta fada a baya ba na matsalar tsaro.

Kaico! an wayi gari ‘yan bani-na-iya suna amfani da duk abin da za su iya wajen jifar junan su da mugayen abubuawan lalata kokarin junan su tare da kokarin dakile tasirin junansu ta hanyar munafurci, makirci domin neman gindin zama da matsayi, da makamantan su. Wanda hakan ya tilasta wasu yin saranda da bayar da gari amma idan siyasar gaba ya samu da neman gindin zama, ko bayan an samu nasara sai ka ga ana bibiyar mutum da sharrin yadda za a lalata duk kokarinshi.

Sannan wani abin takaici ba shugabannin ba ne suke tsara makircin, wasu yardaddun makusanta da suka kware a iya murdiya a kan duk wata nasarar da ba nasu ba ne ya samu, duk wanda shugaba ya ba shi matsayi bi sa jajircewa da kokarin sa ba zai guje wa wannan makircin ba.
Lokaci ya yi da gwamnatin Yobe za ta farka ta haska fitila don ta san irin kalar kowa ta anihi ba rudin da masu kura da fatar akuya ke yi ba.

What's On Your Mind?