Kuran ƙus ! Babu wanda ya kama ni ko ya kai ni kotu – Rahama Sadau

- Advertisement -

Kuran ƙus ! Babu wanda ya kama ni ko ya kai ni kotu - Rahama Sadau

Fitacciyar ƴar fim ɗin Hausa na Kannywood Rahama Sadau ta ce ita babu wanda ya kama ta sannan ba wanda ya yanke mata hukuncin ɗauri a gidan yari.

Rahama ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita a ranar Talata da yamma, bayan da bayanai ke ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta cewa an kama ta an kai ta Kotun Shari’ar Musulunci kan zargin ta da hannu a ɓatancin da aka yi wa Manzon Allah.

Ta ce: ”Ban san daga ina labarin nan ya samo asali ba. Don haka ina kira ga mutane da su daina yaɗa labaran ƙarya marasa makama…”

A makon da ya gabata ne Rahamar ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Tuwita da ke nuna bayanta a buɗe, inda mutane suka yi mata rubdugu da tofin Allah tsine.

Duk da wasu na caccakar jarumar sport da hotunan da ta wallafa, wasu kuma kare ta suka yi.

Bbchausa ta kara da cewa,mafi yawan wadanda suka fito daga yankin kudancin Najeriya na yabon hotunan, yayin da waɗanda suka fito daga arewaci ke suka, inda har wani ya yi kalaman ɓatanci kan Annabi Muhammadu a ƙasan hotunan, lamarin da ya ɗauki wani sabon salo.

Bidiyo: Muneerat Abdussalam Ta Sake Dawowa Musulunci Ga wani Sabon Sako zuwa Ga Kowa Da Kowa

Daga baya jarumar ta fito ta bayar da haƙuri kan abin da masu ɓatancin suka yi, ta kuma goge hotunan gaba ɗaya.

Sai dai duk da haka zancen bai mutu ba don kuwa a ƙarshen makon da ya gabata rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bai wa kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna umarnin ɗaukar mataki kan Rahama, bayan da wani mutum mai suna Lawal Gusau ya kai ƙararta ga ‘yan sandan kan hotuna da ta wallafa ɗin da suka jawo ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

‘Ba wanda ya kama ni’

A cikin jerin saƙonnin da ta wallafa ɗin jarumar ta ci gaba da cewa ta samu saƙonni da dama kan cewa an kama ta tare da yanke mata hukuncin zaman gidan yari a ranar Talata.

”Ni ban samu saƙon gayyata daga ƴan sanda ko sammacin kotu ba. Ina sake jaddada wa masu yi min fatan alheri cewa ina nan lafiya lau kuma babu wata tuhumar shari’a da na samu.”

”Ga masu son mayar da wannan batu wani abu daban da zai jawo rashin zaman lafiya, na roƙe ku bar shi haka..!!!

”Yanzu lokaci ne mai tsanani a gare ni. Ba lokaci ne na yaɗa labaran ƙarya ba. Ina godiya sosai ga waɗanda suka tuntuɓe ni,” in ji ta.

Ta ina zancen ya samo asali?

Da safiyar ranar Talata ne labari ya fara yaɗuwa a shafukan sada zumunta cewa za a gurfanar da jarumar a gaban Kotun Shari’ar Musulunci don tuhumarta da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad

Sai dai har yanzu babu tabbacin daga ina zancen ya samo asali.

An ƙirƙiri maudu’ai da suka haɗa da #Rahama Sadau da #Qur’an da #Islam da #Pretend Information inda aka yi amfani da su sau dubbai.

Muhawarar ta ranar Talata ma dai ta karkata ne tsakanin Musulmai ƴan arewacin ƙasar da Kiristoci daga kudanci masu kare ta.

- Advertisement -