Kura Ta Lafa A Gidan Yarin Kano Bayan Wata Zanga-zanga

0
107

Kura Ta Lafa A Gidan Yarin Kano Bayan Wata Zanga-zanga

Hukumar gidan yari a jihar Kano ta ce an samu daidaito da zaman lafiya a gidan yarin Kurnawa biyo bayan zanga-zangar da fursunoni su ka yi a cikin gidan yarin ranar Alhamis.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar a Kano, DSC Musbahu Kofar-Nasarawa ne ya tabbatar da hakan wa manema labarai ranar Juma’a a jihar Kano.
Su dai fursunonin, an ruwaito cewar solar yi zanga-zangar ne sakamakon matsalar abinci, inda su ka koka akan kalar abincin da ake basu a gidan yarin hadi da karancin sa.
A cikin bayanin nasa, jami’in huldar ya ce tuni aka dakile yunkurin tayar da tarzoma a gidan yarin, wanda hakan ya jefa fargaba da tsoro a zukatan gidajen da ke makwabtaka da gidan yarin.
“Wasu fursunonin solar yi yunkurin tayar da tarzoma a ciki, amman, ma’aikatan gidan yarin tare da sa hannun jami’an tsaro solar shawo kan matsalar,” in ji shi.
To sai dai, Mista Musbahu ya musanta zargin tabarbarewar abinci a gidan yarin a matsayin dalilin zanga-zangar, yana mai cewa, “ Ba matsalar rashin abinci ko tabarbarewar sa ba ne dalilin zangar-zangar, gaskiyar zance shi ne yunkurin kwace haramtattun kayayyaki ne a hannunsuj da ma’aikatan gidan yarin su ka yi ne bai masu dadi ba. Kuma kura ta lafa yanzu an shawo kan matsalar”
Haka kuma, ya bayyana cewar, hukumar gidan yarin ta nada kwamitin bincike domin gano musabbabin zanga-zangar da kuma safarar haramtattun kayayyaki a gidan yarin.

What's On Your Mind?