Kungiyoyin Musulunci Sun Lalubo Bakin Zaren Warware Sabaninsu A Kaduna  

0
41

Kungiyoyin Musulunci Sun Lalubo Bakin Zaren Warware Sabaninsu A Kaduna   

Daga Abubakar Abba,

kungiyoyin addinin Musulunci daban-daban solar hadu cikin inuwa daya domin lalubo bakin zaren kawar da gani-gani da suke wa juna da nufin tabbatar da hadin

A yayin gudanar da taron, an bayyana cewa, akwai wawaken gibi a tsakanin darikun addinin Musulunci daban-daban musamman a Jihar Kaduna wanda shi ne silar haifar da sabani da rashim fahimtar juna a tsakaninsu.

Hakan na kunshe ne a cikin takardar bayan taro da shirin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma na CIPP ya fitar a Kaduna, jim kadan bayan kammala taron bita na kwana  biyu da aka shirya wa Malaman  addinin Musulunci a Kaduna.

Taron tattaunar an gudanar da shi ne a tsakanin mabiya darikun addinin Musulunci da suka hada da, na Izala, Shi’a, Fityanul Islam da sauransu.

Kimanin Malaman addinin na Musulnci na darikun daban daban da suka fito daga karamar hukumar  Kaduna ta Arewa  da wasu makotan yankuna suka halarci taron.

Taron  ya gudana ne a dakin taro na shalkwatar Jama’atul Nasril Islam (JNI)  da ke a Kaduna inda ya samu halartar musulmi daga sassa mabanbanta.

Har Ila yau, a taron wanda cibiyar mabiya addinai mabanta IMC da ke jihar Kaduna ta shirya, an lura da cewa,  akwai karancin ilimi a tsakanin wasu malamai na manyan addinan musulunci,  rashin kwarewa kan wasu fannonin ilimi, da rashin girmama fahimtar  juna da kuma  son ‘yan siyasa.

Takardar bayan taron wacce ta samu sa hannun Jami’in Sadarwa na Cibiyar IMC Hayatu Nura, ta tabo batun yadda wasu malaman addinin Musulunci da ke hakilon neman shugabanci ta halin ko kaka ke amfani da addini don cimma burinsu.

Sun kuma koka kan yadda ake samun karuwar masu tu’amalli da kayan maye da kuma fyade a kasar nan tare da ayyukan daba musamman a tsakanin matasa.

Sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi kungiyoyin addinin Musulunci su tashi tsaye wajen fadakarwa kan illar shaye-shaye,  fyade, zaman kashe wando a tsakanin matasa da kuma sauran kalubale na rashin tsaro da ke addabar alumomin   kasar  nan.

A cewarsu, ya kuma zama Wajibi daukacin kuniyoyin addinai su amince da girmama juna, jurewa zama da juna da girmama fahimtar su da kuma yin wa’azin wanzar da zaman lafiya.

Sun kuma amince da cewa,  ko wanne malamin addinin Musulunci ya yi wa’azinsa kan inda ya fi kwarewa  tare da gudanar da yin bincike domin kara fadada ilimi.

Sun kuma bayar da shawarar a kafa kafar sada zumunta domin sanarwar a kan lokaci  domin dakile dukkan wani rikici ko nuna tsatsauran ra’ayi.

 

What's On Your Mind?