Kungiyar Tallafawa Marayu Ta Ba su Gudummowar Abinci  

0
119

Kungiyar Tallafawa Marayu Ta Ba su Gudummowar Abinci   

Daga Ibrahim Muhammad,

A ci gaba da tallafawa marayu da kungiyar tallafawa marayu da gajiyayyu na Unguwar Gandun Albasa da kewaye suke musamman a cikin watan Ramadan ta raba tallafin  kayan abinci abinci da sutura ga marayu a yankin.

Babban sakataren kungiyar Alhaji Abdullahi Muhammad Gumel ya bayyana cewa kamar yanda aka Saba duk shekara Kungiya ta fitarda kudi N1,80,000,00.ta sayo kayayyaki na abinci da sutura kari akan Wanda suka samu daga jama’a  ba su isa ba. Shi ya sa suka kara fito da kudin suka sai kayayyakin dan rabawa marayu dan ya wadatar.

Ya ce, mutane tsakanin iyayen marayu da marayun da gajiyayyu guda 500 suka amfana da tallafin da aka bai wa iyayen marayu turamen atamfofi aka bai wa ‘ya’yansu yaduka da za su dinka kayan sallah sannan akwai kayan abinci daya hada da shinkafa da wake da taliya da man girki da dawa da tsaki.

Alhaji Abdullahi  Gumel yace sunada tsari da suke bi tuntuni a baya solar raba Gandu da kewaye kashi uku akwai Gandu yamma akwai Useful Tsakiya akwai Gandu Gabas Wanda kowanne suna da wakilai da suke da kididdigar kowane gida na marayu da gajiyayyu da ake tallafawa. Gandu ta tsakiya saboda yawa an rabata gida uku ne bangaren Arewa da tsakiya da bangaren kudu  aka raba kaya gida uku kowane wakili ya dauka haka Gandu gabas Wanda yake ya hada da Kundila da Rumfa suma sunada wakilai da suke rabawa haka ake raba kayan kowa ya sani ana bashi adadin mutane da za a raba musu kayan.

Ya ce, kowane gida za abi akai masa ana baiwa kowane gida lamba da za su zo a basu kayan. Kuma kungiyar ta soma wannan hidima ga marayu ne tun a shekara ta 2002 shekaru 20 kenan suna cikin wannan aiki.Kuma kullum a cikin bukata  suke tunda ana rasuwa marayu suna karuwa a kullum a cikin bukata ake ta tallafi da yakamata ace mutane na bayarwa domin yarane kanana marayu da suke bukatar ilimi Wanda yanzu ma suna kula dasu tun daga Makarantun furamare dana Islamiyya wasu sunje makarantun sakandire Babba da karama wanda yanzu ma akwai wadanda aka Kai manyan makarantu na gaba da sakandire Wanda akwai bukatar kudi. Sannan akwai kulada lafiyarsu ta kaisu Asibiti da saya musu magunguna wani lokaci da biya musu gwaje-gwaje akan lafiya akwai wasu marayu ma da suke kula dasu da sukeda larurar tabin hankali Wanda kusan kowame wata sukan kaisu Dawanau su sayo magani su dawo dasu gida.

Yace suna kulada  da ilimi da lafiyar marayu da nema musu inda zasu koyi sana’a na dogaro dakai wasu na koyon dinki wasu kafinta wasu ana kaisu makarantu da ake koya musu girke-girke dama aikin lantarki da walks. Suma Mata akan basu jari su juya tayin sana’oi su dawo dasu in solar sami nasu ba tareda dora musu komai ba.

Abdullahi Gumel yace ko kwanannan saida wata kungiya ta kawo musu kekunan dinki guda uku suka rabawa marayu guda biyu Mata daya namiji tareda basu jari Sai dai ta bangaren Gwamnati basu sami tallafinta ba.Dan haka yayi Kira ga Gwamnati da fahimci cewa su wakilantane sune idonta a harkokin marayu domin su Solar fitone suna kulada marayu domin su zama yan kasa nagari dan haka yakamata ta kulada irin wadannan kungiyoyi ta zama dasu lokaci lokaci tana jin irin matsalolinsu da bata shawarwari domin wannan tafiyace da kowa Sai yaje ba wanda za’a bari idan an bar yara marayu na gararamba zai iya zama barazana.

What's On Your Mind?