Kungiyar Tabbatar Da Mulkin Karba-karba A Kebbi Ta Zabi Shugabanni

0
93

Kungiyar Tabbatar Da Mulkin Karba-karba A Kebbi Ta Zabi Shugabanni

Kungiyar nan mai fafutukar ganin an dabbaka mulkin karba-karba a Jihar Kebbi ta zabi sababbin shugabanni.

An gudanar da zaben ne a garin Argungu inda aka kasa mukaman gida biyu tsakanin gundumar Kebbi ta Arewa da ta kudu. A gundumar Kebbi ta Arewa aka zabi Alhaji Salisu Namagare a matsayin shugaba, Honarabul Bala Gali Kamba a matsayin Sakataren gudanarwa,  Honarabul Garba Umar Birnin Tudu a matsayin Sakataren kudi sai Alhaji Muhammad Arzika Dakingari (Dan Atto) a matsayin mai bincike.
Daga Kebbi ta kudu kuma  Alhaji Kabiru Muhammed Dabai a matsayin Sakatare, Honarabul Zailani Muhammed a matsayin Ma’aji, Alhaji Alhassan Gwazawa, walwala, Honarabul Abdullahi Muhammed Lamba shi kuma jami’in hulda da jama’a, sai kuma mai bada shawara kan shari’a Barista Yusuf Borodo.

Galadima ya bayyana wadanda suka kulla yarjejeniyar mulkin karba-karba a APC

Zaben shugabannin wannan kungiyar dai ya biyo bayan wadansu tarurruka da aka gudanar a garuruwan Zuru da Argungu a karkashin jagorancin Janar Muhammad Magoro (Murabus).
Da ya ke zantawa da wakilinmu jim kadan bayan kammala zaben, sabon shugaban wannan tafiyar Alhaji Salisu Namagare ya Sha alwashin tafiya tare da kowa ba tare da cin zarafi ko tsangwama ba saboda ba wani Dan siyasa da su ke yiwa wannan fafutukar illa dai burin su bai fin tabbatarda adalcin karba-karba a Jihar Kebbi ba
Ya bayyana cewa ba shakka akwai Jan aiki a gabansu amma dai duk da haka za su yi iya kokarin su na ganin hakarsu ta cimma ruwa, ba sa su yi kasa a gwiwa wajen tuntubar duk wanda ke da rawar da zai taka wajen cimma burin na su.
Ya kuma baiwa al’umma tabbacin za su yi wannan aikin tsakani da Allah kuma kofar karbar shawara a bude ta ke ga kowa ba tare da la’akari da bambancin Jam’iyyar siyasa ko bangare ba da ya ke har ma daga Kebbi ta tsakiya akwai mutanen da ke da sha’awar wannan tafiyar.

What's On Your Mind?