Kungiyar Lauyoyi A Bauchi Ta Bukaci Gaggauta Wanzar Da Shari’o’i

0
55

Kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen jihar Bauchi (NBA) ta danganta jinkiri da ake samu wajen gudanar da shari’a ga rashin hadin kai na masu ruwa da tsaki dangane da lamuran shari’a.

Kungiyar ta zayyana masu ruwa da tsaki cikin harkokin shari’a da suka hada da Alkalai, Masu gabatar da Kararraki, Ma’aikatar Shara’a, Hukumar Tsaro ta ‘Yan Sanda, hadi da Kotuna, tana mai cewar, wajibi ne wadannan masu ruwa da tsaki su wanzar da hadin kai tsakanin su domin ingantuwar aiki.

Shugaban Kungiyar NBA reshen jihar Barista Abubakar Abdulhameed Bununu ya shaida wa ‘yan jarida a garin Bauchi jiya cewar, hadin kai da ake hankoro tsakanin masu ruwa da tsakin zai rage wahalhalun dake kawo jinkiri wajen gudanar da shari’o’i a jihar ta Bauchi.

Kungiyar Lauyoyi A Bauchi Ta Bukaci Gaggauta Wanzar Da Shari’o’i

Bununu ya bayyana cewar, ziyarce-ziyarce da kwamitin Alkalin Alkalai ta jihar Bauchi ke kaiwa gidajen gyara-halin-ka jefi-jefi dake cikin jihar ana yinsa ne da zummar rage cunkoso a wadannan gidaje ta hanyar sakin masu kananan laifuka wadanda kuma gudanar da shari’o’in su suke tafiyar kwam-gaba-kwam baya.

Ministan Sheikh Pantami Ya Wakilci Buhari A Wajan Kaddamar Da Tubalin Gina Jami’ar AS-Salam Global University A Garin Hadejia

Kamar yadda ya zayyana, sakin ire-iren wadannan mutane da ake tuhumar su bisa kananan  laifuka, ya kan sanya su fahimtar cewar, su ma suna da ‘yanchin kasancewa ‘yan kasa, hadi da jijiya na cewar gwamnati tana sane da su a matsayin photo voltaic a ‘yan kasa masu bayar da tasu gudummawa.

Gwamnati ta zage damtse ne wajen ganin cewa, an yi afuwa wa wadanda suke da kananan laifuwa, da biya wa ire-iren wadannan masu kananan laifuka kudaden tara da basu taka kara photo voltaic karya ba, da aka zartar masu, da ba su da halin biya. “A mafi yawancin yanayi, ire-iren wadannan kudade na tara suna kasa da naira dubu hamsin, koma can kasan-kasa”.

Bununu ya ce, ba zai iya fayyace kimanin iren-iren wadannan kudade na tara ba, dake makare a kan wadannan mutane dake cikin gidaje gyara halin ka ba, wadanda a mafi yawancin yanayi Alkalin Alkalai ke biya wa wadannan masu kananan laifuka.

What's On Your Mind?