Kungiyar Jama’atu Ta Yi Tir Da Danganta Pantami Da Mutuwar Yakowa

0
87

Kungiyar Jama’atu Ta Yi Tir Da Danganta Pantami Da Mutuwar Yakowa

kungiyar ‘Jama’atul Nasril Islam (JNI)’ ta yi tir da yadda aka danganta mutuwar marigayi tsohon Gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa da kungiyar da kuma Ministan Sadarwa Dr Isa Pantami.

Sakataren kungiyar ta JNI, Dr Khalid Abubakar, ya sanar da haka a takardar manema labarai da aka taba a Kaduna ranar Juma’a.

Ya kuma kara a cewa, kungiyar JNI karkashin jagoracin Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar III, ta bukaci gwamnatin tarayya da sauran rundunonin tsrao su tabbatar da an gudanar da bincike don gano wadanda suka aikarta wannan laifi na yada karya a tsakanin al’umma.

“Mun yi matukar mamakin ganin yadda wasu mutane ke kokarin ganin solar bata sunan Ministan Sadarwa Isa Pantami sai kuma suka jawo sunan kungiyar JNI a cikin wannan sharri na su, da bayanin sharrin cewa, muna cikin wani shiri da aka yi na kashe Marigayi Yakowa.

“Ya kamata a tababbar da gudanar da bincike mai zurfi, muna kuma yin tir da wanna shirin na jawo mu a cikin wani abin da bamu san hawa ba naked sauka.
“Muna kuma kira ga jami’an staro su gaggauta fara gudanar da bincike don kamawa tare hukunta wadanda suka aikata wannan sharirin,” inji sanarwar.
“Muna kuma addu’ar Allah ya karo mana zaman lafiya a kasarmu Nijeriya ya kuma taimaki shugabaninmu a dukkan mataki,” inji shi.

What's On Your Mind?