Kungiyar Isis Na Duniya Sun shelenta yin Garkuwa da Gwamna Zulum

0
56

Kungiyar ‘yan ta’addan ISIS na duniya ta bayyana daukar alhakkin harin kwanton bauna wa tawagar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum wanda reshenta na yammacin afirka Boko Hatam/ISWAP suka kaddamar masa a hanyar zuwa garin Baga.

Kamar yadda shahararren marubucin nan Datti Assalafy ya ruwaito cewa ,ISIS tayi bayanin cewa tana so tayi garkuwa da Gwamnan Zulum ne ta kamashi da ransa kafin ta dauki mataki kansa, kuma sunyi alwashin cigaba da nemansa har zuwa ranar da burinsu zai cika.

Ubangiji Allah Ka kareshi, Ka haramtawa ISIS samun nasara a kanshi, Ka cika masa burinsa na ganin karshen bayan Boko Haram Amin

Gwamna Zulum yayi alwashin cewa bayan garin Baga Insha Allahu zai wuce ya ‘yanto garin Marte da Abadam kuma ya mayar da ‘yn gudun hijira zuwa gidajensu a wadannan garuruwa nan ba da jimawa ba.

Boko Haram suna da taurin kai, kuma suna da hatsari, duk abinda sukace zasuyi sai solar aiwatar ko da kuwa zasu rasa ransu, hakika suna jin haushin Gwamna Zulum, hakanan manyan maciya amana masu cin amanar tsaron Nigeria suna jin haushinsa saboda yana toshe musu hanyar neman kudi, zasu iya hada baki da Boko Haram su bayar dashi a matsayin hadaya.

HOTUNA: Taron Kaddamar Da Gina Jami’a da gagarumin wa’azin kasa A Hadejia

Datti Assalafy ya kara da cewa,muna jan hankalin Maigirma Gwamna da ya kara tabbatar da karfin tsaron kansa, sannan a duk lokacin da zai ziyarci wani gari inda yake da hatsari to ya fara tura jami’an tsaro suyi clearance operation akan hanya kafin ya biyo baya, sannan ya dinga shiga cikin mota mai sulke wanda bullet mai karfin AA ba zai iya hudawa ba.

Ubangiji Allah Ka kareshi, Ka haramtawa ISIS samun nasara a kanshi, Ka cika masa burinsa na ganin karshen bayan Boko Haram Amin.

What's On Your Mind?