Kungiyar Fararen Hula Ga Gwamna Masari: Ka Gaggauta Biyan Kudin Jarabawar NECO

0
75

Kungiyar Fararen Hula Ga Gwamna Masari: Ka Gaggauta Biyan Kudin Jarabawar NECO

Gamayyar kungiyoyin fararen hula a Jihar Katsina photo voltaic yi kira da babar murya ga gwamnatin jihar Katsina ta da yi duk mai yuwa wajan ganin ta biya kudin jarabarwa NECO ta ‘yan asalin jihar domin ba su dama su cigaba da karatu kamar sauran daliban wasu jihohi.

Wannan kiran yana kunshe ne acikin wata sanarwa da shugaban gammayar kungiyar AbdurRahman Abdullahi Dutsin-Ma ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Katsina.

Kungyar ta ce hankalinta ya kadau so sai da ta ji labarin cewa dalibai ‘yan asalin Katsina har yanzu ba su samu sakamakon jarabawarsu ta NECO ba da suka zauna a shekarar 2020.

https://mobilized9ja.com.ng/an-kashe-dan-sanda-daya-a-yayin-da-zanga-zangar-neman-rushe-sars-ta-rikide-zuwa-rikici-a-wasu-jihohi-Three/

“Abinda muka gani a kan wannan labari shi ne, hukumar jarabawar NECO taki sakin sakamakon jarabawar daliban jihar Katsina saboda rashin biyan kudin da gwamnatin jihar Katsina taki yi kimanin naira miliyan 400 duk da cewa gwamnatin ta bada miliyan 82 da farko” inji sanarwar.

Kazalika kungiyar ta yi bayanin cewa duk da wadancan kudade da aka biya kuma akwai kwakwawar  fahimta tsakanin hukumar NECO da kuma gwamnatin jihar Katsina har yanzu babu labarin sakin sakamakon jabarawar.

A cewar kungiyar hakan ba abinda zai haifar sai jawowa Katsina bakin jini a idon duniya, da jefa ta cikin tsaka da fargaba ga iyayan yara akan makomar karatunsu.

Sai dai kuma kungiyar ta ce akwai iyayen yara da suka biya kudadansu da kansu ta hanyar makarantun gwamnati, ta ce babu adalci da aka rike masu sakamakon jarabawar ‘ya ‘yan su, lallai wannan al’mari zai kara taba mutuncin jihar Katsina ta fuskancin cigaba da kuma ilimi.

Bisa ga haka hadadiyar kungiyoyin fararen hula na kira da babar murya ga gwamnatin jihar Katsina ta yi duk mai yu wa wajan ganin an warware wannan matsala ta biyan kudin NECO ta daliban ‘yan asalin jihar Katsina domin ba su dama su cigaba da karatun kamar yadda saura suka yi a wasu jahohi.

What's On Your Mind?