Ba zamu koma aji ba sai an biya mana bukatunmu – Kungiyar ASUU ta yi tsokaci kan bude makarantu

0
68

Kasa da sa’o’i 24 bayan gwamnatin tarayya ta sanar da bude dukkan makarantu, kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta ce malamanta ba zasu koma makaranta ba sai an biya bukatunsu.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa biodun Ogunyemi, ya tunatar da gwamnatin tarayya da iyayen yara cewa lakcarorin solar shiga yajin aiki ne saboda an ki amsa bukatunsu.

Kungiyar ASUU ta yi tsokaci kan bude makarantu

Yayinda yake tsokaci kan sanarwan bude makarantu, Ogunyemi ya bayyanawa jaridar Solar cewa “Ba mu muka kulle jami’o’i ba. Hakkin gwamnati ne ta bude. Amma kuma hakkinmu ne mu ki karantar da dalibai.”

Ogunyemi ya ce kungiyar ta dade tana yaki da gwamnatin tarayya kan kudaden da ake bukata wajen yiwa jami’o’in Najeriya garambawul domin su kara da manyan jami’o’in duniya.

Recreation da albashinsu kuwa, Ogunyemi ya ce manhajar IPPIS ta haifar da matsaloli da kuma hanyoyin sata da jami’an gwamnati.

(Hotuna) Sanata Goje ya angwance da hamshakiyar GMD ta kamfanin Binani, Hajiya Aminatu

A cewarsa, kokarin tilastawa lakcarori rijista a manhajar IPPIS ba tare da amincewarsu ba ya sa mambobinsu basu samu albashi ba na tsawon watanni uku zuwa takwas yanzu.

“Shin kun san wasu mambobinmu basu samu albashi tba un watan Febrairu 2020. Manhajar IPPIS ba zata iya tafiyar da tsarin biyan albashi a jami’o’i ba.” Ya ce

Ogunyemi ya yi kira ga dalibai da iyaye su kara hakuri da kungiyar saboda ana wannan yajin aikin ne don inganta jami’o’i.

What's On Your Mind?