Kungiyar ActionAid Ta Nemi A Inganta Jindadin ‘Yan Jarida A Nijeriya

- Advertisement -

Kungiyar ActionAid Ta Nemi A Inganta Jindadin ‘Yan Jarida A Nijeriya

Daga Bello Hamza, Abuja

kungiyar ActionAid reshen Nijeriya ta bukaci masu gidajen jarida su tabbatar da suna biyan ‘yan jarida cikakken hakkokinsu.
Shugbar kungiyar a Nijeriya, Ene Obi ta yi wanna kiran a cikin bukukuwan ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya a tattaunawarsa da manema labarai a garin Kaduna ranar Litinin.
“’Yancin ‘yan jarida na daya daga cikin ginshikin mulkin dimokradiya, ya kuma kamata a sama musu yancin in har ana so su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
“Ya kuma kamata masu gidajen yada labarai su tabatar da biyan ‘yan jarida dukkan hakkokinsu,” inji Obi.
Ta kuma nuna rashin amincewarta akan yadda gwamnati da hukumomin da ba na gwamnati ba ke danne hakkokin ‘yan jarida a yayin da suke gudanar da aikin su a Nijeriya, hakan yana kawo cikas ga aikin da ‘yan jaridar ke yi a kasar nan.
Ta kuma tunatar da cewa, gwamnatin Nijeriya ta yi alkawarin kare hakkin ‘yan jarida tare da basu hakkokin su a shekarar 2018, amma kuma abin takaici shi ne gwamnatocin da suka biyo baya solar kasa cika wanna alkawarin.
Daga nan ta kuma shawarci gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki su kara sakewa yan jarida mara tare da biyan su hakkokin su gaba daya.

An Shawarci Al’ummar Musulmi Su Cigaba Da Aikin Alhairi Ko Da Watan Ramadan Ta Wuce
Daga Alhussain Suleiman
Ya da kyau da kuma muhimmanci ga al’ummar musulmi su cigaba da aikata aikin alhairi da suka saba gudanarwa ko da watan azumin mai albarka ta wuce, aikin da suka hada da karatun Alkur’ani mai girma da kuma salloli na nafila da kuma taimakawa marayu da marasa gata da tare da kyauta ta dabi’u.Wannan bayani ya fito ne daga bakin Alhaji Nasiru Hussaini Agalawa Ok.Agur alokacin da yake zantawa sport da kwanaki masu albarka da suka rage a cikin watan Ramadan .
Alhaji Nasiru Hussaini Agalawa Kafin Agurya kara da cewa duk da an kusa kammala Azumin na Ramadan akwai bukatar al’ummar musulmin ka da su gajiya wajen cigaba da addu’a da kuma addu’a acikin kwanakin da suka rage .Malam Nasiru ya ce har yanzu akwai sauran lokaci masu hali su kara himma wajen amfani da dukiyar su wajen taimakawa marayu da marasa gata a cikin watan na Ramadan , sannan akara zage damtse da addu’a domin kasar nan ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali domin har yanzu babu abin da kasar nan take bukata irin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Alhaji Nasiru Agalawa dake gudanar da harkokin kaswuanci a kasuwar Kantin Kwari a Kano, ya ce Azumin Ramadan ta na koyar da juriya da kuma hakurisabodahaka ya zama wajibi mu kasance masu hakuri da kuma juriya alokacin ibada Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya karbi Azumin da al’ummar musulmi ke gudanar wa a cikin kwanakin da suak rage mai albarka na Ramadan

 

 

 

 

 

An Bukaci Musulmi Su Yi Wa kasar Addu’a A Cikin Kwanakin Da Suka Rage Na Ramadan
Daga Alhussain Suleiman
Ganin yadda al’ummar musulmin kasar nan da na Duniya ke shirye shiryen kammala Azumin watan Ramadan mai albarka, har yanzu akwai damar da al’ummar musulmin kasar nan za su dage wajen yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kwanakin da suka rage na kammala watan na Ramadan. Wannan bayani yan fito ne daga bakin Alhaji Murtala Abdullahi da aka fi Sani da suna M A danchanji da ke Kano.
Murtala Abdullahi ya kara da cewa ba bu shakka matsalolin tsaron da kasar nan ke ciki abu ne mai tayar da hankali musamman akan matsalar tsaro amma da yardar Allah idan aka mayar da hankali wajen addu’a kasar n an za tan fita daga matsalarb tsarom da sauran matsalolin da le addabar kasar nan . Da ya juya ga masu hali n da suka taimakawa la’umma musamman marayu da mabukata acikin watan na Ramadan sai ya ce har yanzu ka da su gajiya da irin wannan aikin alhairi su dore ko da watan ta wuce, inji Malam Murtala Abdullahi . Ya ba da misali da yadda wasu ke nuna alhinin su idan aka ce watan na Ramadan ta kusa wuce wa ko kuma ta wuce domin ba dole ba ne mutum ya sa ke ganin wata Azumin Ramadan din mai zuwa.
Ya kuma yi amfani da wannan dama da jinjinawa jami’an tsaron kasar nan akan kokarin solar a samar da tsaro afadin kasar nan, sai yay i kira ga al’ummar kasar nan da su cigaba da baiwa jami’an tsaron hadin kai da goyon baya har Allah ya kaimu karshen matsalolin tsaron da ake fama da shi yanzu haka .
danchanji ya mika sakon gaisuwar ta’aziyar shi ga sarakunan Kano da Bichi, a bisa rasuwar mai babban daki Hajiya Maryam Ado Bayero, ya ce wannan babban rashi ne ga al’ummar kasar nan

 

Fiye Da Fursunan Owerri 1,200 Basu Dawo Ba Bayan Tarzoma
Daga Idris Aliyu Daudawa
Kamar dai yadda mutane suka sani, kwanakin baya ‘yan bindiga solar kai hari gidan gyara halin ka na Owerri, inda daga cikin fursunoni 1,844 da suka tsere daga Hukumar Kula da Gyara halinka ta kasa (NCS),gidan fursunoni na Owerri, wannan kuma biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai wa gidan ranar 5 ga Afrilu, hakan ya sa har yanzu da akwai fursunonin da suka wuce 1, 200 wadanda har yanzu ba a gansu ba.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta sashen Jihar na Owerri Goodluck Uboegbulam, shi ne wanda ya bayyana wa maneam labarai haka a ofishinsa, jiya, cewar kusan fursunoni 600 daga cikin wadanda suka gudu ne suka dawo, ko dai don radin kansu ko kuma ta hanyar sake kamo su da aka yi.A cewarsa, jami’an hukumar ta, tun bayan harin da aka kai ne, sai suka kara sa himma wajen tabbatar da cewa fursunonin da suka gudu solar dawo, kuma irin wannan al’amarin bai sake faruwa ba.
Ya yi kira ga jama’a da su taimaka wajen bada bayanai wadanda za su taimaka masu, da ma har za s yi sanadiyar kamo su fursunonin da suka wuce, domin kasancewar su ba inda ya dace su zama ba, ba karamar matsala hakan zai kawowa al’umma ba.
Kamar dai yadda yayi karin bayanin cewar “daga cikin fursunoni fiye da 1,200 daga cikin fursunoni 1,844 da suka gudu daga inda muke tsare har yanzu ba a gansu ba”. Sai dai kuma kamar yadda ya ce fiye da 600 suk dawo da kansu ko kuma an sake kama su. Amma suna fatan da yawa daga cikinsu za su dawo don ra’ayin kansu saboda kuwa kusan kullum suna dawowa.
Bayan an kai shi harin kamar yadda ya ce solar dauki wasu matakai masu yawa da suka hada da zuwa kafafen yada labarai daban-daban da kuma bin hanyoyin da za mu bi don samun su. Maganar gaskiya,har ma solar kai ga rubutawa majami’u, da kuma shugabannin al’umma da kauyuka; suaka sanar da su illolin da suke tattare da barin fursunonin da ke gudu su boye a cikin al’umma.

 

- Advertisement -