Kungiya Ta Nemi A Samar Da Tsaro Ga Mata Da Yara

- Advertisement -

Kungiya Ta Nemi A Samar Da Tsaro Ga Mata Da Yara

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Hadaddiyar kungiyar cigaban matan Lapai Azza ( Lapai Azza Ladies Improvement Affiliation) ta nemi a samar da ingantacciyar tsaro ga mata da yara duba da irin hare haren ‘yan bindiga da Boko Haram a kasar nan.

Shugabar kungiyar, Amina Mohammed Gulu tayi kiran karshen makon jiya a Minna, inda ta bukaci hukumomi da su dauki matakan gaggawa dan samun bakin zaren walwale matsalar rashin tsaron da ake fuskanta.

Ta bayyana cewar da damar mata an kashe su, kuma an yiwa ‘yayansu fyade, yaran su da aka sace ba zasu iya bayyana wahalhalun da suke ciki ba, ya zama wajibi gwamnati daga sama har kasa, da jami’an tsaro su tabbatar an kawo karshen wannan ta’addanci a kasar nan ba tare da jan kafa ba.

Amina Gulu ta jawo hankalin iyaye mata, matan aure, ‘yaya mata da kannai da yannai mata da suka fito daga Lapai Azza da su hada kai da kungiyar dan kawo cigaba a yankin.

Tace samar da shugabannin daga matakin mazabu zuwa karamar hukuma ya nuna karfin kungiyar wajen wayar da al’ummar karkara muhimman abubuwan cigaba, dan haka ta kalubalance su akan shiga siyasa dan kaucewa mayar da su baya.

A cewarta, ” kungiyar kan ta hade yake wajen wayar da kan matan Lapai Azza dan nuna soyayya da jinkai ga juna, ta hanyar musanyar ra’ayoyi da kuma yin magana da murya daya, dan fuskantar matsalolin ilimi, kiwon lafiya, cigaban yankin da yaki  da talauci da samar da gwamnati mai inganci”.

Tace ” muna horar da muhimmancin zaman lafiya, zaman tare da kyawawan dabi’u, muna wayar da kan iyaye muhimmancin ilimin ‘yaya mata, da kawo cigaban matasa da ya shafi ilimi da horar da su sana’o’in hannu, kasuwanci domin dukkan su tsani ne na gina rayuwar yara masu tasowa har kan jikokin mu da kuma wasu karnin masu tasowa”.

- Advertisement -