Kulawar Da Gwamna Ganduje Ke Baiwa Gaya Na Kara Bunkasa Cigabanta –Hon. Ahmad Tashi

- Advertisement -

Kulawar Da Gwamna Ganduje Ke Baiwa Gaya Na Kara Bunkasa Cigabanta –Hon. Ahmad Tashi

Daga Ibrahim Muhammad,

Shugaban karamar Hukumar Gaya Hon. Ahmad Abdullahi Tashi ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan jahar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda ta silar Gwamnatinsa ne aka dawo musu da Masarautar Gaya wanda ta zame musu abar tarihi da alfahari.

Ya ce suna godewa Allah da Sarki da ‘yan majalisarsa bisa yadda suka fito aka gudanar da idin karamar Sallah karkashin Masarautar Gaya da dinbin al’umma suka halarta na Gaya maza da mata. Ahmad Abdullahi Tashi Gaya ya ce ba za su manta da gudunmuwa irinta mukarraban Gwamna irinsu shugaban riko na jam’iyyar APC na jahar kano.alhaji Abdullahi Abbas da Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo tare da wazirin Gaya sakataren Gwamnatin jihar Kano. Alhaji Usman Alhaji wanda dashi aka yi sallar idi a masarauta wannan ya nuna yanda karamar Hukumar Gaya take samun cigaba kullum.

Shugaban karamar Hukumar na Gaya ya kara da cewa suna alfaharin da ganin wannan cigaba da ake samu a lokacin mulkinsa solar godewa Allah bisa wannan dama daya bashi. Ya ce kananan hukumomi 9 dake karkashin Masarautar Gaya suna gode musu bisa yanda suke bada goyon baya ga Masarautar wanda tunaninsu kullum shi ne na yanda za su kawo cigaban Masarautar.

Ya ce, masarautar Gaya bisa irin goyon baya da kulawa da suke samu daga Gwamnan jahar Kano suna daga kananan hukumomi da suke zaune lafiya a Kano saboda haka suna godewa al’ummar karamar Hukumar musamman malamai da suka tashi gadan-gadan wajen addu’oi da ake masallatai a kan Allah ya kawo zaman lafiya ga Gaya da jahar baki daya.

- Advertisement -