Kudurin Kafa Cibiyar Kiwon Dabbobi Ta kasa Ya Tsallaka Karatu Na Biyu A Majalisar Dattawa

0
74

Kudurin Kafa Cibiyar Kiwon Dabbobi Ta kasa Ya Tsallaka Karatu Na Biyu A Majalisar Dattawa

Daga Abubakar Abba

Majalisar Dattawa ta yi dubiu kan kudurin kafa Cibiyar kiwon dabbobi ta kasa, musaman bisa nufin ganewo, dakile satar shanu da kuma kare dabbobin daga kamuwa daga cututtuka.
Sanata Muhammad Bima Enag ne ya dauki nauyin kudurin, har ila yau, kudurin na da nufin ilimantawa da kuma fadakar da masu kiwon dabbobi da ke a fadin kasar nan, musammnan domin magance rikice-rikicen da ke yawan barkewa a tsakanin Fulani Makiya da Manoma da ke a fadin kasar nan.

Da yake yin bayani a wani karamin zaman da majalisar dattawan ta yi a ranar Talatar dat ta gabata, Sanata Muhammad Bima Enag ya bayyana cewa, kudurin zai taimaka matuka wajen bunkasa fannin kiwon a kasar nan.
“ Wannan kudurin idan ya zamo doka zai taimaka matuka wajen bunkasa fannin kiwon a kasar nan tare da kuma magance rikice-rikicen da suka ki cinyewa a tsakanin Fulani Makiyaya da Manoman da ke a fadin kasar nan”.
Sanata Muhammad Bima Enag ya ci gaba da cewa, “Ina son in kara tunatarr da mu cewa, wannan kudurin ya shallake majalisa ta takwas, sai dai abin takaici, kudurin ba tsallake siradin majalisar da dattawa ba”.
A cewar Sanata Muhammad Bima Enag, kudurin ya zo a kan gaba kuma ina fatan ‘yan uwana ‘yan majalisar, za su goyi bayan wannan kugurin domin ya zamo doka, musamman idan akayi la’akari da irin mahimmancin da yake dashi kan bangaren kiwo da kuma kawo karshen rikice-rikicen da ke yawan aukuwa a tsakanin Fulani Makiya  da Manoman da ke a fadin kasar nan.

“ A gani na kudurin ya zo a kan gaba kuma ina fatan ‘yan uwana ‘yan majalisar, za su goyi bayan wannan kugurin domin ya zamo doka, musamman idan akayi la’akari da irin mahimmancin da yake dashi kan bangaren kiwo da kuma kawo karshen rikice-rikicen da ke yawan aukuwa a tsakianin Fulani Makiyaya da Manoman da ke a fadin kasar nan”.
Sanata Muhammad Bima Enag ya kara da cewa, makukar dabbobin da suka ci gaba da yada cutuukan, hakan zai kuma zamo babbar barazana ga lafiyar ‘yan adam kuma jama’a za su ci gaba da kyamar cin naman na dabbobin.
A cewar Sanata Muhammad Bima Enag, kafa Cibiyar za ta kuma taimaka matuka wajen shigo dabbobi cikin kasar nan, musamman domin kare lafiyar ‘yan kasar nan daga cin naman dabbobin da bas u da lafiya da aka shigo das u cikin kasar nan.
Sanata Muhammad Bima Enag ya kuma bayyana cewa, kafa Cibiyar z ata taimaka wajen samar da kyakwan tsari ga gwamnati da kuma tabbatar da ana kiya ka’idoji wajen kasuwancin  kiwon dabbobi a kasar nan.
Bugu da kari, wannan kudurin, za a kuma tura shi zuwa ga kwamitin aikin nomad a raya karkara  na majalisar da dattawaT, inda kuma kwamitin zai gabatar da na sa rahoton a cikin sati hudu masu zuwa.

kudurin ya dai tsallake karatu na biyu ne a yayin karmin zaman da majalisar ta yi a ranar Talatar da ta gaba.

What's On Your Mind?