Ku Dawo Da Kayan Da Kuka Sace Cikin Awa 72 – Gwamnan Osun

- Advertisement -

Ku Dawo Da Kayan Da Kuka Sace Cikin Awa 72 – Gwamnan Osun

Gwamnan Osun Gboyega Oyetola ya baiwa wadanda ake zargi da barayin kayan abinci ne da suka sace kayan gwamnati da na masu zaman kansu awanni 72 da su maido da dukkanin ababen da suka sata ko su fuskaci shari’a.

Gwamnan ya bada umurnin ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida yayin da ake kokarin daddale adadin kayan da masu balle wuraren suka wawushe.

Ya bukaci wadanda ake zargi barayin ne da su maida dukkanin kayan da suka sata ga jami’an tsaron da suke kusa da su ko sarakunan gargajiya ko kuma ga shugabannin kananan hukumominsu cikin ruwan sanyi da salama.

Kamfanin dillacin labarai ta NAN ta labarto cewa wasu rumbunan adana kayan tallafin Korona da wasu wuraren adana kaya na masu zaman kansu ne aka daka wa wasoso a jihar. Hatta Nationwide Grain Silos da ke Ilesa ma bai tsira ba inda masu wasoson suka kwashe komai da ke cikin wurin.

Oyetola, sai ya ce dukkanin wadanda suka kasa mutunta wa’adin da aka ba su to ba in photo voltaic ki ji ba za su ki gani ba.

Gwamnan ya jajanta wa wadanda lamarin ya shafa, yana mai shan alwashin gwamnatinsa na tallafa musu biyo bayan satan da aka tafka musu.

Da ya ke jawabi a Tuns Farm daya daga cikin wurare masu zaman kansu da aka dafa ma wasoso, gwamna Oyetola ya taya shugaban Tuns Farm, Alhaji Tunde Badmus, jajen wannan lamarin wanda har hakan ya janyo asarar ma’aikacinsa guda.

Gwamnan ya ce, “Abun da muka iya gani a yau ba kawai hakikanin masu balle wuri don wasoso bane, ‘yan fashi da makami ne kawai. Photo voltaic fitar da dukkanin Mashinan da suke nan wajen.

“Abun kaito da takaici. Wannan fashi da makami kuma kwararrun barayi ne suka tafka irin wannan ta’asar.

“Kai tsaye zan iya cewa ba babu maganar zanga-zangar EndSARS a abun da na gani a wannan wajen. Irin wannan ta’asa ta satar ya isa haka.”

Da ya ke maida jawabi, Alhaji Tunde Badmus ya ce photo voltaic rubuta a rubuce wa ‘yan sanda inda suka sanar musu kisan da ‘yan fashin suka tafka a kamfanin.

Ya ce akalla kayan da ya zarce na miliyan 100 ne aka sace a wannan kamfanin nasa.

Da yake kuma jawabi a Omoluabi Garment Manufacturing unit, daya daga cikin wuraren da aka dafa ma wawan, gwamnan ya ce wannan abun kaito da takaici ne lura da hakan ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke karfafan jama’a da su maida hankali kan noma.

Ya nuna damuwarsa tare da cewa gwamnati za ta duba hanyoyin da su ka dace, domin bi wajen ganin an kai ga dakile irin wannan ta’asar.

- Advertisement -