Kowa Ya Fahimci Munafuncin Amurka Kan Kare Hakkin Dan Adam A Rikicin Da Ke Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila

- Advertisement -

Kowa Ya Fahimci Munafuncin Amurka Kan Kare Hakkin Dan Adam A Rikicin Da Ke Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila

Daga CRI Hausa

Yanzu kowa ya fahimci munafuncin kasar Amurka kan kare hakkin dan Adam bisa rikicin da ke faruwa a tsakanin Palasdinu da Isra’ila. Amurka ta sha sukar wasu kasashe a fannin kiyaye hakkin dan Adam, yayin da ta kau da kai daga yadda ake keta hakkin Palasdinawa, har ma take rura wutar rikicin.

Kamfanin dillancin labaru na Sputnik na kasar Rasha ya ruwaito a yau cewa, ya zuwa yanzu Palasdinawa 217 solar rasa rayukansu a rikicin, ciki har da kananan yara 63. Wane mataki gwamnatin Amurka ta dauka ta jin haka? Babu abin da ta yi, sai nuna wa Isra’ila goyon baya, har ma ta yi shelar cewa, Isra’ila na da ikon kare kanta.

Ta kuma hana kwamitin sulhun MDD ya fitar da wata sanarwar hadin gwiwa don tsagaita bude wuta a tsakanin Palasdinu da Isra’ila. Jaridar Washington Put up ta ce, a farkon wannan wata, gwamnatin Amurka ta sanar da majalisar dokokin kasar cewa, za ta sayar wa Isra’ila makaman da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 735. Ma iya cewa, Amurka ta nuna cewa, babu ruwanta a cikin rikicin da ke faruwa a tsakanin Palasdinu da Isra’ila, sai ma kara rura wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amurka ta dade tana aikata abubuwa maras kyau a Gabas ta Tsakiya bisa son kai tare da yin danniya. Miliyoyin musulmai solar rasa rayukansu sakamakon matakan da Amurka ta dauka a kasashen Afghanistan, Iraq, Syria da sauran kasashe, tare da keta hakkin dan Adam na goman miliyoyin musulmai. Amma ‘yan siyasan Amurka solar mai da hankali kan hakkin dan Adam na musulman jihar Xinjiang ta kasar Sin. Lawrence Wilkerson, tsohon kanar a rundunar sojan Amurka ya bayyana a fili cewa, batun kabilar Uygur ta Xinjiang, wata makarkashiya ce da Amurka ta kulla, a yunkurin hana ci gaban kasar ta Sin.

‘Yan siyasan Amurka suna yunkurin biyan bukatunsu ta fannin siyasa bisa hujjar fakewa da batun kare hakkin musulmai a sassa daban daban na duniya. Tun tuni kasashen duniya suka dawo daga rakiyar salon Amurka na kiyaye hakkin dan Adam. Nan gaba Amurka ba za ta ci gaba da kiran kanta mai rajin kiyaye hakkin dan Adam ba. (Tasallah Yuan)

- Advertisement -