Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai

0
28

Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yankewa mataimakin kwamishanan yan sanda, Okubo Aboye, da bakanikensa, Niyi Afolabi, hukuncin daurin rai da rai kan laifin amsan motar sata.

Hakazalika Alkalin kotun, John Adeyeye, ya yankewa wasu mutane biyar hukuncin daurin shekaru 5 a Kurkuku kan laifin garkuwa da mutane, TVC ta ruwaito.

Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai

Anyi garkuwa da wani hakimi a jihar Adamawa

Wadannan masu garkuwa da mutane sune Solomon Ayodele Obamoyegun (39), Femi Omiawe (40), Damilola Obamoyegun (20), Bose Sade Ajayi (30), George Fortunate (35), Chukwuma Nnamani (22) da Sunday Ogunleye (45).

Aboye, wanda mataimakin kwamishanan yan sanda ne ACP, da bakanikansa solar saya motar sata daga hannun masu garkuwa da mutane.

Yayinda yanke hukuncin, Alkali Adeyeye yace, “Garkuwa da mutane don amsan kudi abu ne wanda ya zama ruwan dare ba a jihar nan kadai ba, amma a Najeriya gaba daya.”

“Da kotun nan ta yi abin kunya idan bata hukunta wadanda ake zargi da hukunci mai tsauri ba.”

A karar da aka shigar, “solar aikata laifin ne a Ado Ekiti inda suka yi garkuwa da wani mutum Moses Ajogri kuma suka kwace masa mota kirar Toyota Hilux mai lamba, Lagos APP 509 BK.”

What's On Your Mind?