Fyade: Kotu ta Kori Soja Daga Aiki, ta Yanke Masa Hukuncin Shekaru 5 a Gidan Yari

0
61

Wata kotun rundunar soji da ke zama a Maiduguri jihar Borno a ranar Laraba, ta kori wani soja daga aiki tare da yanke masa hukuncin zaman shekaru 5 a gidan yari.

Sojan mai suna kofur, Aliyu Yakubu an kama shi da laifin yin fyade a ranar 13 ga watan Yulin 2020 kuma an gurfanar da shi a gaban kotun sojin.

Kamar yadda soja mai gabatar da kara ya sanar, Yakubu ya ja yarinya mai shekaru 13 zuwa wani kango a ranar 1 ga watan Yulin 2018 a Bama inda ya ci zarafinta kafin ya yi mata fyade.

Kotu ta Kori Soja Daga Aiki, ta Yanke Masa Hukuncin Shekaru 5 a Gidan Yari

Yarinyar ta sanar da kotun cewa, sojan yayi mata fyade ne yayin da ta bar gidan kanwar mahaifiyarta za ta tafi gidansu.

“Ya tambayeni inda zani kuma na sanar masa, daga nan ya ja hannuna yace in bi shi,”lauya Aminu Mairuwa, mai mukamin Kaftin ya sanar kamar yadda yarinyar tace.

“Ya ja ni zuwa wani kango ta bayan tsohuwar gidan yari sannan ya rufe min baki saboda ina ihu.

“Ya fito da wuka tare da yin barazanar kasheni. Bayan ya yi min tsirara sai ya kasa shigata. Daga nan ya tambayeni ko an taba saduwa da ni, amma nace a’a. A take ya shigeni ta karfi.

(*5*)Yadda Arewa24 Ta Dauki Nauyin Faifan Bidiyon Safarau

“Bayan kammala fyaden, ya yi amfani da bulo wurin fasa min kai kuma ya bar ni ban san halin da nake ciki ba,” cewar Mairuwa.

Daga bisani jama’a solar ga yarinyar inda aka dauketa zuwa asibiti. Bayan farfadowarta ta sanar da abun da ya faru kuma ta gane sojan.

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta tsare wani matashi, Solomon Okon, na tsawon wata guda bayan ya yi yunkurin kashe kansa. Solomon ya sha wani sinadari mai guba da niyyar ya kashe kansa saboda ya rasa aikinsa.

Lamarin ya faru ne a cikin watan Agusta bayan an damkawa Solomon takardar sallamarsa daga aiki a wani asibiti mai zaman kansa.

Wani makusancin Solomon ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda solar tsare shi kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban kotu.

What's On Your Mind?