Korona: Mutum 47,290 Ne Aka Yi Wa Riga-kafin A Bauchi  

- Advertisement -

Korona: Mutum 47,290 Ne Aka Yi Wa Riga-kafin A Bauchi   

Daga Khalid Idris Doya,

Adadin mutane dubu 47,290 ne zuwa yanzu aka samu nasarar yi musu allurar rigakafin Korona na AstraZeneca domin kariyan kai daga kamuwa da annobar nan ta Korona a rukunin farko na yin rigakafin ga jama’an Bauchi wanda aka samu nasarar cimma kashi 84 cikin 100 na adadin da aka yi harsashen musu tun da farko.

 

A karin farko na rigakafin an maida hankali wajen yi wa jami’an kiwon lafiya, jami’an gwamnati, sarakuna da shugabannin addinai, inda aka samu amsar rigakafin daga wadannan bangarorin hannu biyu-biyu.

 

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aliyu Maigoro Muhammad shi ne ya shaida hakan yayin kaddamar da fara yin rigakafin karo na biyu ga wadanda aka yi musu tun da farko bayan makonni 9.

 

Maigoro ya yi bayanin cewa wadanda aka yi harsashen musu a zango na farko solar yi umumu wajen fitowa domin amsar rigakafin ba tare da wani tangarda ba a dukkanin fadin jihar.

 

Har-ila-yau, ya kuma an kuma samu rashin fitowa sosai ga jama’an da suke shiyyar kudancin jihar musamman Katagum wajen amsar wannan rigakafin, ya horesu da su sauya hakan domin alfanun da rigakafin ke da shi ga lafiyarsu.

 

A cewarsa, da zarar mutum ya samu amsar rigakafin karo na biyu, bincike ya nuna cewa ya sha daga kamuwa da cutar kwata-kwata, muddin aka samu bin ka’idar yin na farko da na biyu wa mutum lallai ba zai kuma kamu da cutar ba.

 

A lokacin da yake kaddamar da fara yin rigakafin karo na biyu, Gwamna Bala Muhammad wanda ma shi ne aka fara ma yi, ya bayyana cewar kididdiga ya nuna jihar Bauchi tana na gaba-gaba wajen samun adadin masu amsar rigakafin wanda ya nuna hakan a matsayin nasara.

 

Gwamnan sai ya roki gwamnatin tarayya da ta kara hada kai da jihohi domin a cewarsa gwamnatocin jihohi solar fi kusa da al’umma domin ganin an samu nasarar fito da dabarun da kowa zai samu rigakafin nan na Korona.

 

Bala wanda kuma ya nuna rashin jin dadinsa bisa yadda al’umman Kiristoci suke kaurace wa amsar rigakafin a jihar, ya nuna cewa hakan ba zai taimaka ba domin ba za su ke samun zuwa ziyarar wurin ibada a Isra’ila cikin sauki ba muddin basu amince aka musu rigakafin ba.

 

Ya ce, duk da cewa adadin yawan kiristoci a jihar ba wai wani yawa ke da shi ba, amma hakki ne a kansa ya tabbatar da kare musu lafiya domin su ma solar zabeshi, don haka ne ya nemi shugabanninsu da su din ma da su maida hankali wajen amsar rigakafin domin kariya daga annobar.

 

Daga nan gwamnan ya jinjina wa sarakuna da limamai a bisa hadin kai da wayar da kan jama’ansu da su yi ta yi wajen ganin an samu yin rigakafin yadda ya dace ya nemi su kara hakan.

 

Gwamnan wanda ya amshi rigakafin tare da mataimakinsa Baba Tela, matarsa Hajiya Aisha Bala da sauran jami’an gwamnatin jihar.

 

A nasa fannin, shugaban kwamitin yaki da cutar Korona a jihar, Sanata Baba Tela, ya jinjina wa al’umman jihar Bauchi bisa hadin kai da suke bayarwa na fitowa domin amsar rigakafin na korona a karo na farko, yana mai cewa wadanda suka fi amsar rigakafin solar kunshi jami’an lafiya, jami’an gwamnati, sarakuna, da sauran wadanda aka yi harsashen za su fara amsa.

 

Tela wanda shine mataimakin gwamnan jihar ya bada tabbacin cewa rigakafin zai isa duk wani lungu da sako na jihar inda ya nemi jama’a da su cigaba da basu hadin kai domin samun nasarar yi wa kowa rigakafin.

 

Sannan ya jinjina wa gwamnan jihar a bisa hadin kai da goyon baya da yake baiwa kwamitin yaki da cutar wanda a cewarsa hakan ne ma asasin samun dukkanin nasarorin da suke kan samu a halin yanzu.

 

Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Rilwanu Mohammed, ya bayyana cewar a karon farko din an yi wa kaso 97 rigakafi a jihar wanda hakan ke nuni da Bauchi tana kan gaba wajen amsar rigakafin Korona a duk fadin kasar nan.

- Advertisement -