Korona: Gwamnati Ta Sake Rufe Wuraren Shakatawa Da Holewa A Fadin Kasar Nan

- Advertisement -

Korona: Gwamnati Ta Sake Rufe Wuraren Shakatawa Da Holewa A Fadin Kasar Nan

Daga Idris Aliyu Daudawa

Gwamantain tarayya ta sake rufe wuraren shakatawa da holewa, wannan kuma duk da niyyar hana yaduwar cutar Korona ce a Nijeriya.

Bugu da kari kuma gwamnatin ta sake dawo da hakan a dukkanin Jihohin Nijeriya 36 tare da Abuja babban birnin tarayya.

Shugaban sashen aiki na kwamitin Shugaban kasa akan cutar ta Korona, Dokta Mukhtar Mohammed, shi ne wanda ya bayyana wadannan sababbin matakan wadanda za su fara aiki daga karfe goma sha biyun dare na ranar Talata.

Ya ce wuraren shakatawa da holewa za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai abinda hali ya yi tukuna.

Yayin da yake yin bayanin na cewar ba tafiye- tafiye zuwa wasu wurare aka hana ba, amma kuma ya bada shawarar sai dai kawai tafiya wadda take da matukar muhimmanci, zuwa kasar waje,  za a iya yi , ko ita ma duk sai an bi dukkan ka’idojin da suka kamata  abi.

- Advertisement -