Korar Ma’aikata:  Za A Tsunduma Yajin Aiki A Kaduna 

- Advertisement -

Korar Ma’aikata:  Za A Tsunduma Yajin Aiki A Kaduna 

Ma’aikatan Jiragen sama Da Na kasa Da Na Lantarki Za Su Bi Sahu

Daga Maigari Abdulrahman,

Ma’aikatan gwamnati da na kanfanoni a Jihar Kaduna ciki har da na wutar lantarki solar fara yajin-aikin gargadi ranar Asabar.

A makonnin baya ne, kungiyar kwadago reshen Jihar ta ayyana zuwa yajin aikin a kan nuna rashin amincewa da jin dadin da matakin gwamnatin Jihar na korar ma’aikata.

kungiyar ma’aiakatan wutar lantarki, ta bi sahun sauran ma’aikata na shiga yajin aikin,”Bisa umurnin kungiyar kwadago na tsayar da ayukka a Kaduna cak, daga ranar Asabar,ku dauke wutar Kaduna GABAdAYA,” in ji shugaban kungiyar a cikin sanarwar da su ka fitar.

Ya kuma umurci ma’aikatan da su tabbatar cewa Jihar Kaduna ba ta samo wuta daga makwaftan Jihohi ba na kusa ko na nesa a kan kowane dalili.

Mista Ajaero  ya yi gargadi da cewa, “Duk wanda aka samu, mutum ko wani ofishi da taka dokar, to za a hukunta su bisa taka umurnin kungiya.”

Bacin ma’aikatan lantarki, haka su ma ma’aikatan jirgin sama za su tsuduma yajin aiki a jihar yau Lahadi domin nuna goyon baya ga ma’aikata, kamar yadda kungiyar ta sanar jiya Lahadi.

Ma’aikatan jirgin sama dai solar hada da kungiyar matuka jirgin sama ta kasa, kungiyar tashoshin jirgin sama ta kasa da kuma kungiyar ma’aikata da kwararru na jirgin sama, kamar yadda su ka bayyana a cikin wata sanarwar da gamayyar kungiyoyin su ka fitar ranar Asabar

Wasu daga cikin wadanda su ka bayyana shiga yajin aiki daga gobe Litinin, akwai ma’aikatan jirgin kasa, ma’aikatan kananan hukumomi, da kuma malaman jami’oi.

A watan Aprilu ne gwamnan jihar El-Rufa’I ya bayyana kudurinsa na korar ma’aikata a jihar, a kan dalilin rashin kudi ga gwamnatinsa. Inda ya ce, kaso mai yawa na kasafin jihar yana tafiya ne ga ma’aikatan

A cewar sa. Matakin korar ma’aikatan ya zama dole duba ga karancin kudin jihar, rage ma’aikata zai ba gwamnati damar anfani da kudin wurin bunkasa rayuwar sauran al’umma, in ji shi.

- Advertisement -