Kokarin Da Uwargidan Gwamnan Nasarawa Ke Yi Na kwato Hakkin Mata

0
110

Kokarin Da Uwargidan Gwamnan Nasarawa Ke Yi Na kwato Hakkin Mata

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule sunanta ya yadu a yankin Arewa ta tsakiya fiye da sauran matan gwamnanonin yankin.
Tauraron Uwargidan Gwamnan ya tsaya a tsaye sakamokon  kururuwan da tayi na yaki da dubban mazaje marasa tausayi masu kwadayin abin duniya.
Wadanda suka kudduri aniyar yada muguwar fasadi ta hanyar yiwa yara kanana fyade.
Da wadanda ke bautar da yara kanana ta hanyar safara ko aikatau daga karkara zuwa biranai. Da masu cin zarafin mata.
Uwardidan Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Silifat Abdullah Sule ta kada gangan yaki da masu cinzarafi ta kowani bangare.
Hajiya Silifata Abdullah Sule a wani taro da ya gudana a zauren taro na Matasa mai suna (Ibrahim Abacha Youth Heart) dake Lafia ta gudanar da jawabi a gaban fitattun matan jihar da suka halarci taron a kan gwada al’adu na girkegirke.
Ta ce ” na rantse da Allah duk wanda na samu labarin an kama shi da laifin yiwa raya fyade ko dan waye kuma komin matsayinshi da ni da tawagana za mu isa gurin ba za mu kyaleshi ba har sai an hukunta shi daidai da lefinshi”.
“Ba zan zura ido ina kallo ana walakanta yaran mata ana yimasu Fyade da miyagun ayyuka ina kallo ba, alhalin Allah ya bani dama a matsayina na matar Gwamna ina da dama na kwacewa duk wata mace hakinta a jihar Nasarawa. ”
“A duk lokacin da na samu labarin halinda yara kanana suke ciki masamman wadanda akyiwa Fyade sai hankalina ya tashi naji kamar yarana ne dana haifa a cikina.” Inji Hajiya Silifat Abdullah Sule.
Ta kara da cewa, “Yaran Talakawa yarana ne, yaran masu kudi yarana ne, yaran Musulmai yarana ne, yaran Kirista yarana ne, kai har ma da wadanda ba su da addini saboda na haifi yara nasan zafinsu dole na san zafin na wadansu.”
Ganin cewa uwargidan gwamnan ta zama mai fada da cikawa babu batun turawa zuwa da kai yafi aike ya sanya mazaje da dama masu tunanin aikata irin wannan suka shafawa kansu ruwa.
Yanzu haka a jihar Nasarawa da zarar an ga namiji da karamar yarinya cewa ake yi “ka yi a hankali saboda Hajiya Silifat Abdullah Sule tana nan igiya na hannun ta ka sha dauri.”
Wani mazauni garin Jos ya shaida cewa da zarar an kama wanda ya aikata fyade cewa ake da a Nasarawa ne da ka shiga tarkon Hajiya Silifat ta yi maka daurin goro.
Tun daga lokacin da Uwargidan Gwamnan ta yi wannan yekuwar ta kuma yi kukan kura ta cika hannu da wanda yayiwa yar karamar yarinya yar wata uku Fyade ta tura shi zuwa gidan maza ya tarar da masu aiki irin tashi, mutane suka tabbatar Hajiya Silifat da gaske take yi.
Wasu yankuna na Abuja har gargadi ake wa masu cin zarafin mata da miyagun aiki ana sanar dasu cewa Matar Gwamnan Nasarawa tana kallonku. Kuma ba sani ba sabo.
Wannan kokarin nata ya sanya Masarautan Lafia ta karramata da Sarautan (Giwan Matan Jihar Nasarawa)
Yanzu sunan Giwar Mata ya mamaye ko ina ya rufe sunan Silifat.
Sarkin Lafia mai Shari’a Muhammad Sidi Bage Shugaban Majalisar Sarakuna ta jihar Nasarawa shine da kanshi ya nada Hajiya Silifat Abdullah Sule wannan Sarauta ta Giwan Mata.
Da bakinshi ya ce ta cancanta a kirata da Sarautan Giwan Matan Jihar Nasarawa saboda rawar da ta taka ko take takawa na yaki da takeyi da miyagu masu cin zarafin mata birni da karkara.
Ya ce; “Giwan Matan tayi abubuwan da suka cancanta ne ya sanya aka ba ta wannan mukami mai girma. Tana gudanar da ayyukanta a kan abubuwan da suka shafi matsayin mata da ganin cigaban mata ta hanyoyin dogaro da kai.
Baya ga wannan Sarautan Giwan Mata Hajiya Silifat Abdullah Sule ta samu mukamai daban-daban a masarautu da sauran kungiyoyi masu zaman kansu saboda kokarin da take yi na taimakawa mata ta hanyar ganin su zama masu dogaro da kai.
Sau dayawa kungiyoyi masu zaman kansu ko kuma Gidauniya wato (NGO) sukan kawo mata lambar yabo sakamakon wannan rawar da take takawa na taimakawa mata.
Hajiya Silifat Abdullah Sule takan yi tattaki zuwa Asibiti inda take taimaka wa Jarirai sabbin haihuwa tare da iyayensu a gurare da dams cikin jihar Nasarawa.
Hajiya Silifat Abdullah Sule tayi rawar gani ta hanyar taimakawa mata marasa mazaje wato zaurawa da mazajensu suka rabu dasu ko wadanda mazajensu suka mutu suka barsu da yara kanana.
Haka zalika tana abin a zo a gani wajen taimakawa mata marasa galihu da tsofaffi wadanda shekarunsu ya yi nisa. A kullum tana kokarinta wajen samar da kungiyoyin hadinkan mata saboda cigaba da kuma tabbatar da zaman lafiyan jihar Nasarawa.
Hajiya Silifat Abdullah Sule ta kan yi wa mata bayani cewa dole sai kansu ya hadu a ko’ina, ta hanyar samar da kungiyoyi babu bambamci, ta hakane za su samu cigaba da matsayi a kowani Gwamnati.

What's On Your Mind?