Kofin Zakarun Turai: Watakila A Buga Wasan Karshe A Ingila

- Advertisement -

Kofin Zakarun Turai: Watakila A Buga Wasan Karshe A Ingila

Daga Abba Ibrahim Wada

Ranar Laraba hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa za ta fayyace ko ya kamata ta mai da wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League zuwa babban filin wasa na Wembley dake London.

Tun farko an tsayar da ranar 29 ga watan Mayu, domin buga wasan karshe a filin wasa na Istanbul, amma dokar shiga kasa tsakanin kasashen domin hana yada cutar korona za ta kai tsaiko.
A jiya Litinin hukumar ta Uefa ta yi wani zama da gwamnatin Burtaniya da mahukuntan kwallon kafar Ingila kan wurin da ya kamata a yi wasan karshen a gasar ta Zakarun Turai a karshen wannan watan.

kungiyar Chelsea da ta Manchester Metropolis ne daga Ingila za su buga wasan karshe a gasar ta Champions League ta bana sannan tuni aka gargadi magoya baya daga Ingila cewar ba za’a bari su shiga Turkiya ba, sakamakon dokar hana yada cutar korona tsakanin kasa da kasa.
Hakan ne ya sa hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bukaci a yi wasan a katafaren filin wasa na Wembley dake babban birnin kasar ta Ingila, tun da dai karawar ta ‘yan kasa daya ce za’a buga.

Dokar Burtaniya ta tanadi duk wanda ya ziyarci kasar dake da hadarin kamuwa da cutar korona, idan zai koma gida sai ya killace kansa a otal din da gwamnati ta amince da shi na kwana 10.

Wannan killacewar za ta shafi ‘yan wasan da za su buga gasar cin kofin nahiyar Turai da ya kamata a fara daga 11 ga watan Yuni kuma tun farko hukumar ta Uefa ta tsara bai wa magoya bayan kungiyoyin biyu tikitin kallon wasan karshen four,000 kowacce a fafatawar da aka tsara yi a Istanbul.

- Advertisement -