Ko Wane Hali Kananan Yara Ke Shiga Bayan Sun Rasa Mahaifansu?

0
95

Ko Wane Hali Kananan Yara Ke Shiga Bayan Sun Rasa Mahaifansu?

Tare da Basira Sabo Nadabo,

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicce mu mutane, sa’annan ya sanya mu mafifita a bayan kasa.

Ina so in dan yi tsokaci akan maraici da kuma halin da marayu ke shiga bayan mutuwar uba, musamman wanda ke kula da tarbiyya da ci da sha da kuma tufatar da ‘ya’yan sa. Na sani kowa akwai irin jarabawar da Allah ya yi masa. Shi maraya Allah ya jarabce shi da rashin iyaye hakan ya sa suke fuskantar kalubale iri-iri.

Saboda haka zan yi wannan tsokacin ne domin mutanen da ba su san kunci da zafin da maraya ke ji ba a zuciyar shi  yau su sani.  Domin komin kankantar yaro ya san mecece kulawa, ya kuma san dadin soyayya. Ba yaro ba kawai, hatta babban mutum baligi akwai wani yanayi da zai riske shi ya ji yana da-na-sanin ina ma ace mahaifinsa na da rai? To ina ga karamin yaro kuma?

Rashin iyaye na sa marayu su fuskanci kalubale masu yawa wanda yake janyo musu tangarda a dukkan al’amuran da suka shafi rayuwa. Saboda rashin samun tarbiyya, abinci, tufafi, gurin zama da ingantaccen ilimin addini da na boko!

Abinci yana kasancewa abu ne wanda aka fi bukatuwarsa a kullum sau uku ko kasa da haka, amma su marayu samu sau daya ma yakan gagare musamman wanda ba shi da gata, saboda babu wani tsayayyen namijin da yake kulawa da cinsu, hakan ya sa ba sa samun isashshen abincin da yake gina musu jiki kamar wadanda suke da iyaye maza suke samu.

Maraici na hana su samun ababen extra rayuwa wanda iyaye ke saya wa ‘ya’yansu. Kamar su indomie, bobo, biscuits, lemu, ayaba, kankana, alawar yara, shinkafa da nama ko kifi da sauran su. Wadannan abubuwan da na zayyana wasu suna ganin ba komai ba ne a gurinsu amma a gurin maraya abu ne mai girma!

Tufafi ya kan yanke wa maraya har ya kasance suna sa kaya yagaggu saboda rashin hali. Saboda haka ya sa suke sanya tufafi wanda ya samu ba wanda ransu yake so ba, a wajen bikin sallah ko abinda ya shafi wata hidima!

Ta fuskar muhalli kuwa, wato wajen kwana yakan gagara a gurin marayu saboda za a samu wasu solar gaji gidajen amma ba shi da amfani saboda zubar ruwa, wasu kuma kwanukansu ne ya daga, wasu kuma gidan ba shi da maraba da kango, wasu daga ciki kuma iyayensu solar rasu solar bar su a gidan haya ba sa iya biyan kudi saboda rashin masu taimaka musu. Hakan ya kansa wa maraya rayuwa a cikin kunci da rashin walwala!

Ita kuwa tarbiyya idan aka rasa mahaifi takan kwace don iyaye mata suna da rauni. Har takai an samu matsalar da zai kawo lalacewar tarbiyyar marayu, kamar shaye-shaye, sata da yawan zinace-zinace da sauransu. Saboda rashin uba wanda yake taimakawa gurin tarbiyyar ‘ya’ya maza da ‘ya’ya mata!

Ilimi a gurin marayu yana samun tangarda da zarar solar rasa uba. Domin hidimar karatu da sauran dawainiyya yana kan uba ne don ita uwa taimakawa kawai take yi, idan kuma uwa ta rasa mataimaki to za a samu matsalar da zai kawo rushewar rayuwar ‘ya’ya har su zama abin kyama a cikin al’umma. Wadannan na daga cikin dalilin da ya sa marayu ke bukatar samun nagartaccen ilimi domin su taimaki kansu, iyaye mata da sauran al’umma bakidaya!

Rashin uwa babban rashi ne ga da ko ‘yar da ta rasa mahaifiyyarta a kananan shekarun da ba su gaza uku zuwa sama ba, suna shiga mummanan halin da ko solar girma a gurin matar uban da ba ta san martaba da darajar marayun da aka bar mata ba, ko da kuwa gurin ‘yar’uwar yaran da suka rasa mahaifiyar su ne hakan ke sa su shiga gararin maraici mara galihu.

Matar uba wata mace ce wacce ke rike da ‘ya’yan mijinta bisa dalilin rashin uwar ‘ya’yansa, sai rikonsu ya koma hannun matar ubansu. Babu tsoron Allah da tausayi a zuciyarta haka za ta yi ta azabtar da yaran don kawai suna matsayin ‘ya’yan mijinta.

Babu nagartaccen ilimin Boko da na Muhammadiyya a gurinsu kuma ba ta damu da nema musu ilimin ba don kawai solar kasance marayu ‘ya’ya a gurin mijinta.

Matar uba ita ce take tarawa ‘yar yarinya wanke-wanke da diban ruwa ba tare da la’akari da karancin shekarunta ba.

Takan tura ta waje siyo kayan miya in kuma biyar ta bata ta ce dole sai ta dawo mata da kudinta ko gurin waye ta samo mata, ba ta damu da wanda zai ba ta ba kudin ko ta amso kudin ba. Ita dai kawai ta kawo mata cikon kudinta.

Ba sa koshi da abincin matar uba kuma haka za su yi hakuri saboda solar gwada fadar ba su koshi ba ta zane su hadi da gargadin duk wanda ya fada wa Baba in ya dawo za ta yanka shi.

Wani a unguwarsu yana janta dakin shi ya yi lalata da ita ya ba ta alawar tsinke amma tana tsoron fada wa matar uba domin ba ta janyota jikinta ba. Babu lura ko kulawa har akai mata fyade saboda rashin kular matar uba.

Ta tafi talla kudi ya bata, amma ta ce duk inda za ta nemo ta je ta nemo kuma ta fita ta dawo da kudin amma ba ta tambayeta inda ta samo ba saboda ‘yar ba ‘yar da ta haifa a cikinta ba ne, shi ya sa ba ta damu da ta lalacewarta ba. Wannan fa duk Saboda gudun duka tare da hanata abinci ya sa ta kasa fada mata abinda dan makobcinsu yake mata.

Tana fita da talla za ta tafi dakin saurayinta ya saye duka ita kuma ta ba shi jikinta. In ta dawo gida da kudi har da uwar riba matar uba ta ce gobe ma ki koma inda ake siyan kayan nan saboda uwarki ba ta bar miki ko cokali ba.

 

Da ga karshe ina fatan alkhairi ga masu ba da gudummuwa da taimakon marayu a duk in da suke a fadin duniyar nan. Ya Allah ka kara mana ni’imar rayuwa, hakuri da masu nuna kulawa ga marayu!

Ya Allah ka sa rayuwar maraya ta zama abar kwatance a fadin duniyar nan. Ya Allah ka sa marayu su samu ingantaccen ilimin da za su tallafi rayuwar maraya!

Ya Allah ka hana kuncin duniya da na lahira a zukatan masu taimakon marayu da masu niyyar taimakawar. Ya Allah ka sa albarka a duk abinda suka taba ko suke da niyyar yi!

A karshe ina yi wa iyaye huduba da su riki maraya a tamkar dan cikinsu da suka haifa, su ma ‘ya’ya ne; idan ka faranta ran maraya Allah zai faranta ranka kuma Ya kara maka/miki albarka a dukkan lamuranka.

 

 

What's On Your Mind?