Kishin Kasa Da Dogaro Da Kai A Nijeriya

- Advertisement -

Kishin Kasa Da Dogaro Da Kai A Nijeriya

Gina ‘yan kasa ta fuskacin akidar kishin kasa da dogaro da kai su na daga cikin manyan tubalan ci gaban kowace kasa a fadin duniyar nan, kana kuma jigon da zai taimaki al’ummar kasar wajen dorata bisa ingantacciyar turbar yanci da diyauci. Ta sakamakon hakan ne zai ga samun sadaukakun yan kasa ma su zuciya da karsashin bai wa al’ummarsu gurbi mai kyau a zukata, kuma cike da fata nagari, hada hannu wuri guda don samar wa kasar kyakkyawar makoma, wadda babu nadama ko da-na-sani tattare da ita.

 

Saboda sai an samu sadaukakkun yan kasa masu kishinta da ingantacciyar soyayya sannan a samu kai wa ga manufa madaukakiya, wanda a karshe za ta kai ga cimma muradi, wanda idan ya hadu da dogaro da kai, zai bai wa yan kasa karsashin da zai karfafa musu gwiwar zabar yi wa kasar su hidima a kankin kansu; babu tilasta wa ko tunanin wani abu, kuma cike da nishadin cire tsammanin samun sakamako dangane da duk girma ko wahalhalun da su ke yi wajen bunkasar kasar su, da abinda bai kai kimar abinda su ka bayar ba. Har wala yau, hakan zai taimaka wajen dorewar ci gaban da su ka gina da hannun su da bayar da kofa ga wadanda su ka cancanta.

 

Bugu da kari, a duk lokacin da wadannan muhimman turaku (kishi da dogaro da kai) su ka samu gindin zama a zukata, zai kai yan kasa a fagen alfahari da ganin kimar abinda su ka yi fafitikar gina wa da hannun su tare da kaffa-kaffar yin aiki tukuru wajen tarairaya da tanadar hazikakan mutanen da za su ci gaba daga inda su ka tsaya don dora wa daga inda su ka tsaya- ta hanyar yin tsinkayen samar da ingantattun manufofi, tsare-tsare da dokokin da za su karfafi manyan gobe. A wannan fage ne kasashen da suka ci gaba su ka yi wa masu tasowa zarrar ciyar da al’ummar su gaba a cikin yanayi na karsashi mai kunshe da alfaharin yadda su ka sadaukar don habaka kasashen su.

 

A hannu guda kuma, masana a fannin ilimin zamantakewa da halayyar dan Adam solar yi fashin baki mai fadi dangane da hanyoyi da matakan da ya dace kowace kasa ko al’umma su bi wajen don taimaka wa wajen samar da kishin kasa da dogaro da kai ga yan kasa. Haka zalika kuma, abu ne sananne kan cewa kishi da dogaro da kai ginshikai ne daga cikin manyan dabi’un da suka gina halayyar dan Adam tare da zaburarwa a turbar ci gaba, haka kuma rashin su baki daya ko daya daga cikin su, babbar tawaya ce da nakasa ga mutum, sannan rayuwa babu wadannan dabi’un tamkar gangar jiki ce babu ruhi; ka ga kenan abu ne mai wahalar gaske muta ta hau titi babu injin, sai dai ayi ta turawa.

 

Har wala yau, masana solar bayyana matakai 10 kan kishin kasa, wanda solar hada da, fahimtar ita kanta kalmar “kishin kasa”, wanda ta haka za ka fahimci kana kan turbarta ko ka kuskure?Sai kuma bayar da gudumawar ka a sha’anin ci gaban kasa da karkata kan kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar ka fiye da na kowace kasa a duniya, bayar da gudumawa a sha’anin tsaron kasa tare da samun dawamamen zaman lafiya da aiki wajen tsabtace muhalli da bashi kariya daga canjin yanayi da gurgusowar hamada.

Sauran solar hada da kasancewa mai alfahari da kasarka, sanya al’ummar kasarka a zuci tare da fata ta gari mai cike da yan uwantaka da son juna, ka zama mai kokarin biyan haraji ko sauke wasu nauyukan da suka hau kanka don ci gaban al’ummarka da shiga ayyukan taimakon kai-da-kai don tallafa wa gajiyayyu da maras galihu a yankin ka da kasa baki daya a karshe da mutunta abubuwan da suka kunshi martabar kasarka da al’ummar cikinta a kowane yanayi.

Matukar kishin kasa da dogaro da kai ya samu gindin zama a zukatan yan kasa, za ka tarar alkiblar kowane dan kasar ya karkata wajen fadi-tashin nemo hanyoyin da zai bayar da tashi gudumawa domin ya taimaki kasarsa da al’ummarsa, sannan babu mai zaman dirshan ko zuba ido kan arzikin da kasarsa ta mallaka cike da burin ya kandami nashi rabo, ya ginu a hankalin shi cewa dukiyar kasa ta kowane dan kasa ce, kuma tanadinta ya dace ayi ba watanda ba. A tunanin al’ummar irin wadannan kasashe shi ne tattali da tanadin abinda kasar ta mallaka don ci gaba tare da shiri ga ya’yansu masu zuwa; ba handame dukiyar kasa ba.

 

A kasashen da Allah ya azurta da ni’imar kishin kasa da al’ummarta, tunaninsu kulli-yaumin shi ne kasar ba daidaikun wasu mutane ba, sannan a shirye kowane yanki yake ya yi aiki kafada da kafada da dan uwansa wajen cimma muradu da manufifin da kasa ta doru a kai a tafarkin ci gabanta. Haka kuma, ba kasafai kabilanci da bangaranci ko masu ci da addini ke samun kasuwa ba, balle samun damar raba kan yan kasa wajen cimma burin kashin kai. Sannan kowa da kowa ya yarda ayi aiki wuri guda a karkashin dokoki da manufofi fiye da daidaikun wasu mutane komai girma da kimarsu.

 

kasar da kishi da dogaro da kai ya zauna daram, mutum ya na samun girma da daukaka ne idan ya kasance a sahun gaba dangane da abinda ya shafi bin dokoki da tsare-tsaren ci gaban kasar, kana da juya wa duk mai kokarin kawo cikas ga ci gabanta ko kokarin raba kawunan yan kasa ko yi kasa zagon kasa, wanda ta dalilin haka ne abu mai sauki wajen bin matakan dakile matsaloli masu muni da kawo cikas a kasa: irin su cin hanci da rashawa, sakaci wajen kin buyan haraji, yi wa dokokin kasa karan-tsaye. Sannan da aiki cikin gaggawa wajen daukar matakai da gano matsaloli tun kafin su gagara.

 

A bangare guda, ta la’akari da halin da tarayyar Nijeriya ta tsunduma a ciki, na sukurkucewar shugabanci, tabarbarewar tsaro, solar samo asali ne daga rashin kishin kasa da akidar dogaro da kai a zukatan yan Nijeriya. Wanda ko shakka babu ba a haka aka hallici kasar ba, face wasu abubuwa ne su ka rinka faruwa har aka kai ga wadannan dabi’un solar kau; ko kasa ko sama. Wanda idan za a tambayi mai karatu ne: “Ya matsayin kishin kasa da dogaro da kai a tsakanin yan Nijeriya?

- Advertisement -