Kisan Sojoji A Benuwai: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Gwamna Ortom

0
61

Kisan Sojoji A Benuwai: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Gwamna Ortom

Daga Maigari Abdulrahman,

Fadar shugaban kasa ta nuna rashin jin dadi a kan kalaman gwamnan Jihar Benuewai Samuel Otom ga Buhari biyo bayan kisan sojojin Nijeriya da kuma farar hula a jihar.

Babban mataimakin shugaban kasa kan harkokin labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja.

A cewar sa, babu wata gwamnati da za ta yi farin ciki da irin wannan al’amari na kisan sojoji da farar hula da ke sansanin ‘yan gudun hijira.

Garba Shuhu ya bayyana cewar, Buhari na kaduwa matuka da kasha-kashen da ke faruwa a Nijeriya, ba ma Benuwai kadai ba.

“Shugaban kasa Buhari ya yi rantsuwar kare dukiyoyi da rayukan al’aumma, kuma yana aiki tukuru don tabbatar da hakan.”

“Ko ma su means eke haddasa wannan rikice-rikicen, koma a ina ne su ke sai solar fuskanci hukuncin laifin aikata wadannan miyagun ayukkan,” in ji Buharin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Shugaban kasa Buhari ya yi amannar banbance-banbancen addini, al’ada ko kabila ba illa ba ne, sai dai ma alheri da alfanu ga kasar.”

“Mu kan tuhume ‘yan mulkin mallaka da laifin rarraba da mulkin kama karya a lokacin mulkin mallaka. A yau, shugabanni ne ke aikata wancan aikin rarraba da bangaranci tsakanin addinai, yankuna, kabilu da al’adu. “

“Mafitar Benuwai, da ma kasar bakidaya tana tattare da zaman lafiya ne da juna, kiyaye doka da oda, da kuma bin tsarin dokoki, ta haka ne kadai za a iya samun cigaban da ake fata.’

Garba Shehu ya bayyana cewar, shugaban kasa Buhari zai kara matsin lamba ga jami’an tsaron Nijeriya na ganin cewa solar tsayu da aikinsu na kare dukiyoyi da rayuwar al’umma.

Sanarwar ta yi nuni da cewar,da hadin kai ne tsakanin gwamnatocin jiha da ta tarayya ne za a iya samun nasarar da ake muradi, a kan haka, ya yi kira ga gwamna Otom da ya hada kai da gwamnatin tarayya don ganin an samar da zaman lafiya a jihar.

“Za a iya samun wannan idan a ka aje son rai gefe, a kuma muhimmantar da rayuwar al’umma birbishin komai. Gwamnatin da mutane ta zaba, to ya kamata ta dauke su d amuhimmanci ba akasin haka ba,” ya fada.

Daga karshe, Garba Shehu ya isar da sakon jajen Buhari ga iyalai, ‘yan uwa da wadanda abin ya shafa. Haka kuma, ya kara yin kira ga ba jami’an tsoro hadin kai a aikinsu na samar.

What's On Your Mind?