Kira Ga Mata Da Su Kare Mutuncinsu

- Advertisement -

Kira Ga Mata Da Su Kare Mutuncinsu

Daga Yusuf Shuaibu

Cikakkiyar kamalar mace tana da alaka ne zuwa ga ababe guda biyu, yanayin mu’amalarta da kuma irin tufafin da ta ke sawa. Sai dai galibi ana yawan samun matsala da su wajen sanya tufafi musamman recreation da abin da ya shafi hijabi, galibi wasu ba su damu da shi ba. Su dai damuwarsu shi ne, ya za a yi su rika bayyanar da wasu sashi na jikinsu tahanyar yafa gyale a gefen kafadarsu. Gyale da mace ke amfani da shi wajen rufe mata tsaraicinta, baya daga cikin mayafin da ke rufe tsaraicin mace da kyau.

La’akari da rashin kaurinsa kuma ba yalwatacce ba ne, sannan da zarar solar yafa shi a jikinsu yakan kwanciya ne a kiran jikinsu tahanyar fidda zahirin sifar jikinsu musamman kirjinsu. Baya ga haka, galibi bai wuce Iyakar kugunsu tare da ya cika ka’idar hijabi ba. Amma mafi yawancin mata shi suka dauka a matsayin hijabi kuma suke amfani da shi.
Duk tarbiyyar ‘ya mace indai tsarecinta zai rika bayyana Koda tana da haddar kur’ani a kayinta hakika ba ta da tarbiyya kuma da sannu iliminta zai zama hujja a kanta wanda daga nadama ne za ta yi. Domin mayafi yana amsa sunansa a matsayin hijabi ne idan ya cika yalwatacce kuma mai kauri ta yadda idan mace tana tafiya ba zai rika bayyanar da wasu bangaran jikinta. To Amma galibi ba sa duba wannan inganci, su dai damuwarsu su yi amfani da gyale wanda zai dunga bayyana surar jikinsu. Kuma iyaye suna ganin ‘ya’yansu na aikata wannan fasadin amma bai dame su ba, wannan babban kuskure ne wasu iyaye suke aikitawa.

Lallai bai kamata mace mai tarbiyya ta dunga saka kayan da za su iya bayyana surar jikinta, wanda wannan yana haddasa yawan fasadi da barna a bayan kasa. Dan haka, ‘yar’uwa ya kamata ki gane tsaraicinki ba abin nunawa a gari ba ne, domin babu abin da yake da kima a jikinki kamar tsaraicinki, wato guraben da Suke da matukar tasiri wajen fusata sha’awar mutum su ne wuri mafi kima da kuma daraja a jikinki, domin su suke jagorantar mutuncinki a rayuwarki.

La’akari da cewa, mahangar mutanen kirki a kan ‘ya mace shi ne, kamalarta na matantaka wato budurcinta shi ne wuri mafi tsada da mutumin kwarai ke son mace ta kiyaye shi daga abin da zai gurbata mata shi, domin cikar kamalarsa shi ne kwarin kiwar duk wanda ta zo gunki da niyyar aure. ‘Yan’uwa mata sai a yi kokarin kiyayewa. Allah ya bayar da iko.

- Advertisement -