Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Ake Siyasantar Da Harkokin Wasanni

- Advertisement -

Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Ake Siyasantar Da Harkokin Wasanni

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa cewa, kasarsa tana adawa da yadda wasu kasashe suke siyasantar da harkokin wasanni.

Madan Hua ta bayyana haka ne jiya Alhamis lokacin da take mayar da martani, sport da yunkurin wasu ’yan siyasar Amurka dake neman yin amfani da gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da kasar Sin za ta shirya a farkon badi, wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar ta Sin.

Hua Chunying ta ce, “Matakan kare hakkin bil-Adama da Amurka take ta ikirari, abin kunya ne.” Tana mai cewa, ’yan siyasar Amurka ba su da wani iko na zargin kasar Sin sport da batutuwan da suka shafi kare hakkin bil-Adama. Shigo da batun siyasa, babu abin da hakan zai haifar, face illata moriyar ’yan wasa daga kasashe daban-daban da za su fafata a gasar. ’Yan siyasar Amurka dai, suna neman yin amfani da wannan batu, don biyan bukatansu na kashin kai.

Amfani da gasar Olympics don neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da sunan batutuwan kare hakkin bil-Adam, ba zai taba yin nasara ba, kuma ba zai samu goyon bayan kasashen duniya ba.

A don haka, Madam Hua ta yi nuni da cewa, idan aka kalli batun kare hakkin dan-Adam, ta fuskar ko dai tarihi ko shaidu na zahiri, to, ’yan siyasar Amurka ba su da ’yancin furta kalaman da ba su dace ba sport da kasar Sin, har ma su rika zargi ba tare da gabatar da kwararan shaidu ba. A don haka, ya kamata su sake nazari a kai.

Jami’ar ta kasar Sin ta ce, “Idan kananan kabilun Amurka suka zo kasar Sin, suka kuma kalli Xinjiang, Na yi imanin cewa, za su yi sha’awar zama Sinawa a wannan zamani”. (Ibrahim Yaya)

- Advertisement -