Kasar Sin Ta Sanar Da Kakaba Takunkumai Kan Wasu ‘Yan Birtaniya Da Kamfanoni

0
89

Kasar Sin Ta Sanar Da Kakaba Takunkumai Kan Wasu ‘Yan Birtaniya Da Kamfanoni

A yau Jumma’a, Kasar Sin ta sanar da kakaba takunkumai kan wasu mutane da kamfanonin kasar Birtaniya.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya fitar, ta ce Birtaniya ta yi gaban kanta wajen kakabawa wasu Sinawa da kamfanoni takunkumai, tana mai dogaro da abun da ta kira batun take hakkin bil Adama a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Sanawar ta ce, matakin da Birtaniya ta dauka bisa karairayi da bayanan bogi, ya keta dokokin kasa da kasa da ka’idojin huldar kasa da kasa, kana tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan Sin, haka kuma ya illata dangantakar kasashen biyu.

Yan Siyasa Ne Kan Gaba Wurin Lalata Tarbiyyar Matasa, Inji Janar Abdulsalam

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta aike da sammaci ga Jakadan Birtaniya dake kasar, domin gabatar da korafinta da kuma bayyana adawarta, tare da yin Allah wadai da matakin.

Bugu da kari, sanarwar ta ce kasar Sin ta kuduri niyyar kare cikakken ‘yancinta da tsaro da muradunta na ci gaba, tare da gargadin Birtaniya da kada ta ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba. Idan ba haka ba, Sin za ta kara mayar da martani. (Fa’iza Mustapha)

What's On Your Mind?