Kasar Sin Ta Bayyana Adawarta Da Daftarin Diflomasiyya Da Japan Ta Fitar

0
71

Kasar Sin Ta Bayyana Adawarta Da Daftarin Diflomasiyya Da Japan Ta Fitar

Daga CRI Hausa

Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta soki Japan tare da bayyana adawarta, dangane da abun da ta bayyana a matsayin kuskure mai tsanani da matakin mara ma’ana da Japan din ta dauka na yayata abun da take kira da “barazanar Sin”.

A martaninta dangane da daftarin diflomasiyya na shekarar 2021 da Japan ta fitar a ranar Talata, ma’aikatar tsaron Sin ta bakin kakakinta Wu Qian, ta ce daftarin ya soki kasar Sin tare da bata mata suna, baya ga yin katsalandan cikin harkokinta na gida.

Da yake tsokaci dangane da sashin da ya tabo batun kudin da Sin take kashewa kan ayyukan soji, Wu Qian ya ce kasarsa na bin hanyar neman ci gaba cikin lumana, da tsarin tsaron kai da kuma tsare gaskiya da yin komai a bayyane dangane da karfin sojinta, da kudin da take kashewa kan ayyukan sojin.

Ya ce cikin shekaru 30 da suka gabata har zuwa yanzu, abun da Sin take kashewa tsaron kasa bai kai kaso 2 na alkaluman tattalin arzikinta ba, wanda ya gaza kai wa adadin na manyan kasashen duniya, da kuma matsakaicin matakin kaso 2.6 na duniya.

Har ila yau, Kakakin ya ce matsayar Sin kan tsaron sufurin ruwa a bayyane take, kuma tsibirin Diaoyu da sauran rassanta, wani bangare da ba za a iya rabawa da kasar Sin ba. (Fa’iza Mustapha)

What's On Your Mind?