Kasar Sin Na Kokarin Nazarin Rigakafin Sabon Nau’in Kwayar Cutar COVID-19

0
80

Kasar Sin Na Kokarin Nazarin Rigakafin Sabon Nau’in Kwayar Cutar COVID-19

Daga CRI Hausa

Kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin ta bude taron dandalin masana kimiyyar likitanci na shekarar 2021 jiya Asabar a birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke gabashin kasar Sin, inda Zhong Nanshan, mamban kwalejin ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, yanzu kasar Sin tana kokarin nazarin allurar rigakafin sabon nau’in kwayar cutar COVID-19.
Mista Zhong ya kara da cewa, tantance wadanda suka kamu da cutar a kan lokaci, tare da killace su ba tare da bata lokaci ba, muhimmiyar hanya ce ta hana yaduwar annobar ta COVID-19 a tsakanin mutane, wadda take taimakawa kasar Sin samun nasarar dakile da kuma kandagarkin cutar a cikin gida. A ganin sa, yanzu abin da kasar Sin ke sa lura a kai shi ne batun bullar sabbin nau’o’in kwayar cutar. Sin tana rubanya kokarinta wajen nazarin allurar rigakafin sabon nau’in kwayar cutar COVID-19.
A cewar masanin, mai yiwuwa ne bambancin kwayoyin halittar mutane yana daya daga cikin muhimman dalilan da suka sanya wasu ke saukin kamuwa da cutar ta COVID-19, wasu kuma kan yi fama da mummunan alamun cutar. Yanzu haka ana gudanar da nazari kan lamarin. (Tasallah Yuan)

 

What's On Your Mind?