Kasar Sin Na Karfafa Kudurin Kare Ikon Mallakar Fasaha Domin Bunkasa Ci Gaba Mai Inganci

0
89

Kasar Sin Na Karfafa Kudurin Kare Ikon Mallakar Fasaha Domin Bunkasa Ci Gaba Mai Inganci

Daga CRI Hausa

Hukumar lura da kare ikon mallakar fasaha na kasar Sin NIPA, ta ce kasar na daukar matakan karfafa kudurorin kare ikon mallakar fasaha, domin tabbatar da bunkasa ci gaba mai inganci, karkashin shirin ta na raya kasa na shekaru biyar biyar, tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
Shen Changyu, shugaban ofishin na NIPA, ya bayyana yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Lahadi cewa, Sin za ta bunkasa samar da kudade, da dabarun sakayya kan samar da ikon mallakar fasaha. Za ta kuma nace ga samar da ci gaba mai nagarta, da ba da kariya, da karfafa gwiwar al’umma wajen samar da ikon mallaka don ingantattun fasahohi.
Kaza lika, an shigar da burin samar da shaidun ikon mallakar fasaha daga kirkire kirkire kan dun mutane 10,000, a matsayin alama da za ta tabbatar da nasarar tsarin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, wanda hakan zai ingizi burin samar da inganci a fannin, maimakon samar da tarin hajoji kawai.
Shen ya kara da cewa, a bana Sin ta daga zuwa matsayi na 14 a jerin kasashen duniya dake kan gaba wajen neman ikon mallakar fasaha, kuma ita ce ta daya daga cikin kasashe masu matsakaicin samun kudaden shiga, kamar dai yadda hukumar WIPO mai lura da fannin ta tabbatar.
Jami’in ya ce a bara, Sin ce kan gaba, wajen amfani da tanadin yarjejeniyar WIPO, ta hadin gwiwar ikon mallakar fasaha, inda kasar ta mika bukatu a fannin da suka kai 69,000. (Saminu)

 

What's On Your Mind?