Kasar Sin Na Kara Kokarin Raya Harkar Yin Allurar Rigakafin Cututtuka Masu Yaduwa

0
79

Kasar Sin Na Kara Kokarin Raya Harkar Yin Allurar Rigakafin Cututtuka Masu Yaduwa

Daga CRI Hausa

Baya ga kokarin da take yi na yiwa jama’a allurar rigakafin cutar COVID-19, kasar Sin ta zuba makudan kudade don raya harkar samar da allurar rigakafin cututtuka masu yaduwa iri-iri.
Taken mako na karshe na watan Afirilu, wato daga ranar 24 zuwa ranar 30 ga watan, shi ne “Makon allurar rigakafin cututtuka na duniya”. An kebe wannan mako na musamman ne, domin neman raya harkar yi wa jama’a allurar rigakafin cututtuka masu yaduwa, don kare masu shekaru daban daban daga cututtukan da ka iya haddasa rashin lafiya. A ganin masanan ilimin kiwon lafiya, allurar rigakafin cututtuka ta taka muhimmiyar rawa a kokarin kare lafiyar bil-Adam, da raya harkokin zaman al’umma.
A nata bangare, kasar Sin na ta kokarin zuba karin kudi ga aikin yi wa jama’ar kasar allurar rigakafin cututtuka masu yaduwa. Ban da wannan kuma tana kokarin tinkarar wasu kalubalolin da suka kunno kai.
Feng Zijian, shi ne mataimakin darektan cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin. Ya bayyana a wajen wani dandalin tattaunawa da Asusun Bil Gates ya kira a jiya Talata cewa, allurar rigakafin cututtuka masu yaduwa na taka rawar gani a fannin kare lafiyar al’ummar duniya, da tabbatar da ci gaban harkokinsu. Ya ce,
“Cikin matakan kare lafiyar jama’a, yin allurar rigakafi shi ne mafi muhimmanci. Aikin yana taka muhimmiyar rawa a kokarin kare lafiyar jikin dan Adam, da tsawon rai, gami da ciyar da harkokin al’umma zuwa gaba. Duk wani kokarin da ake yi na jaddada muhimmancin yin allurar rigakafi ga yunkurin kare lafiyar jama’ar kasashe daban daban, ba zai wuce kima ba.”
Feng ya kara da cewa, kasar Sin tana kara zuba kudade ga aikin yi wa jama’a allurar rigakafi. A bara kudin da kasar ta zuba a wannan fanni ya zarce dalar Amurka miliyan 617. Ta wannan hanya, aikin kandagarkin cututtuka na kasar ya samu nargartaccen sakamako. A cewar Feng,
“Mun kawar da cutar agana a tsakanin shekarun 1950 zuwa 1960. Daga baya mun bullo da tsarin yi wa jama’a allurar rigakafin cututtuka kamar yadda aka tsara a karshen shekarun 1970, bisa goyon bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO, da Asusun tallafawa kananan Yara na UNICEF, da kungiyoyi da gwamnatocin kasashen Amurka, da Japan, da Australiya, da dai sauransu, suka nuna mana. Ya zuwa shekarar 1995, mun dakile yaduwar cutar shan-inna a kasar Sin. Kana a shekarar 2007 zuwa 2008, mun sanya rigakafin sankarau, da ciwon hanta na nau’in A, da kurajen lagwada, da hangum, cikin shirin yi wa jama’a allurar rigakafi na kasa. Ban da wannan kuma, muna kokarin kirkiro sabbin alluran rigakafin cututtuka. Yanzu nau’ikan alluran rigakafi da muka samu suna da yawa. Ban da wasu allurai kalilan, yawancin alluran rigakafi da ake samu a duniya, muna da su.”
Sai dai, Mista Feng ya jaddada cewa, har yanzu akwai wasu sabbin ayyuka da kalubalolin da aikin yi wa jama’a allurar rigakafin cututtuka na kasar Sin ke fuskata, misali sanya karin sabbin alluran rigakafin cututtuka cikin tsarin kasar na yi wa jama’arta allurar rigakafi. Feng ya ce,
“Za mu ci gaba da kokarin kawar da cutar kyanda da ta kurajen lagwada, da kiyaye wani yanayin da ake ciki na magance yaduwar cutar shan-inna, musamman ma kokarin magance sake shigar cutar cikin kasar Sin. Kana za mu rage yaduwar ciwon hanta nau’in B, don kawo karshen cutar dake addabar mu. Sa’an nan wani aiki mai matukar muhimmanci shi ne, a sanya tsarin yi wa jama’ar alluran rigakafin cututtuka na kasa ya kunshi karin sabbin alluran rigakafi. Har yanzu akwai babban gibi tsakaninmu da wasu kasashe, a fannin sanya sabbin alluran rigakafin cututtuka cikin tsarin rigakafin cututtuka na kasa, musamman ma ayyukan baiwa yara karin sabbin alluran rigakafi, da sanya aikin yi wa jama’a allurai dake shafar karin baligai, da dai sauransu. Duk wadannan ayyuka na da muhimmanci sosai.”(Bello Wang)

What's On Your Mind?