Karyar Garkuwa Da Kai Ya Sanya dalibin Jami’ar ABSU Cikin Komar Hukuma

- Advertisement -

Karyar Garkuwa Da Kai Ya Sanya dalibin Jami’ar ABSU Cikin Komar Hukuma

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Jami’an tsaro na cikin gida na Jami’ar jihar Abia, Uturu (ABSU) solar kama wani dalibi mai karatun kimiyar siyasa na jami’ar, George Nnamdi, da ake zargi da yin karyar garkuwa da kansa don neman kudi a wajen iyayensa.

Jaridar MOBILIZED9JA ta karshen mako ta tattara cewa, ya aika wa abokiyarsa da sako a da misalin karfe three na safiyar ranar Juma’a cewa wasu mutane shida dauke da bindigogin AK47 ne suka sace shi tare da wasu dalibai uku.

Bayan wannan, budurwar mai suna Religion Godson, daliba a matakin digiri na 300 na jami’ar jami’ar ta sanar da cibiyar sadarwar, wanda nan take ta fara aiki kuma ta kama shi a maboyarsa.

A nasa martanin, yayin gabatar da wanda ake zargin, babban jami’in tsaro (CSO) na jami’ar, Kwamandan rundunar Sojin Ruwa, ThanksGod Ebulobi (mai ritaya) wanda ya jagoranci binciken ya tabbatar da faruwar lamarin.

CSO din ya bayyana cewa, majalisar dattijan jami’ar ba da jimawa ba za ta dauki matakin da ya dace a kan wanda ake zargin tare da dokoki da ka’idojin da ke jagorantar ayyukan ta.

A martanin da ya mayar, Nnamdi, wanda ya ce yana so ya yi wa abokiyar nasa kawanya ne, ya ci gaba da cewe, ba shi da wata niyya ta aikata hakan kuma ya nemi gafara kan tashin hankalin da ya jawo wa jami’ar.

A halin yanzu, magatakardar jami’ar, Acho Elendu, ya ba da sanarwa a kan lamarin, yana cewa mataimakin shugaban jami’a (VC), Farfesa Onyemachi Ogbulu ya yi Allah wadai da aikin dalibin.

Sanarwar, wacce aka aike ta hanyar sakon E-mail ta wani bangare ta bayyana cewa, “Mataimakin Shugaban Jami’ar ya gargadi daliban da su dauki karatunsu da muhimmanci kuma su guji irin wadannan munanan ayyuka kamar yadda doka za ta identical su.”

Idan za a iya tunawa, jami’ar ta kasance cikin labarai ne a makon da ya gabata bayan sace wasu dalibai mata tare da wasu da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka sace su a kan hanyar Uturu zuwa Okigwe, amma an sake su kwanaki kadan.

- Advertisement -