Sukar Buhari: Karon Farko Hadimin Ganduje Ya Magantu Bayan Dakatar Da Shi

0
38

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje dai ya dakatar da hadimin nasa ne saboda sukar shugaba kasa Muhammadu Buhari.

Saluhu Tanko Yakasai ya mika sakon godiya ga abokan arziki da suka kira shi don yi masa jaje. Hadimin na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda aka dakatar, S, ya yi martani a karon farko bayan dakatar da shi.

Ganduje dai ya dakatar da Yakasai ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Oktoba sakamakon sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi kan rundunar tsaron SARS.

Karon Farko Hadimin Ganduje Ya Magantu Bayan Dakatar Da Shi

Yakasai ya mika sakon godiya ga masoya bisa irin kaunar da suka nuna masa bayan labarin dakatarwar nasa ya bayyana.Tsohon hadimin na Ganduje a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter ya ce ya ji dadin kulawar da jama’a suka nuna masa har cikin zuiyarsa.

“Ina mika godiya ta ga dukkanin mutanen da su ka goya mani baya a jiya, musamman wadanda su ka kira, ko su ka aika mani sakonni ta kafofi dabam-dabam.” “Abin ya yi mani yawa sosai, na yi kokarin mayarwa da kowa amsa amma na kasa aikata hakan. Nagode sosai har cikin zuciyata.”

Za Mu Cigaba Da Tallafa Wa Mata Da Kayan Sana’o’i, Cewar Matar Gwamnan Bauchi

A wani labarin kuma, korarren kwamishinan Ma’aikatar ayyuka da ababen additional rayuwa na Jihar Kano, Mu’azu Magaji (Dan Sarauniya) ya yi magana akan dakatar da Tanko Yakasai, mai bada shawara na Musamman akan harkokin yada labarai ga Gwamna Ganduje. Magaji ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Fb, inda yace an dakatar da Yakasai. Kamar yadda ya wallafa a shafinsa ranar Lahadi, “Gaskiya ban ji dadin dakatar da Salihu Tanko Yakasai da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi ba.

“Salihu amintacce ne ga Gwamna Ganduje. Ban ji dadin fitarsa ba. Allah ya zaba masa mafi alkhairi!” in ji Dan Sarauniya.

What's On Your Mind?